Farar shinkafa babu miya ake bamu sau 1 a rana, Wadanda suka kubuta daga hannun miyagu

Farar shinkafa babu miya ake bamu sau 1 a rana, Wadanda suka kubuta daga hannun miyagu

  • Halima Falalu-Umar mai shekaru 10 ta bayyana yadda ta tsere daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna
  • Ta bayyana yadda suke basu farar shinkafa babu ko miya kuma sau daya a rana lokacin da suke hannunsu
  • Halima ta samu nasarar tserewa tare da kanninta guda biyu; Bashir Nura-Umar mai shekaru 7 da Khadija mai shekaru 7

Kaduna - Halima Falalu-Umar mai shekaru 10, ta tsere daga hannun masu garkuwa da mutane a sansaninsu dake Kaduna ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka yi ta basu farar shinkafa babu miya sau daya a rana tun da suka sacesu.

Halima ta samu ta tsere tare da ‘yan uwanta; Bashir Nura-Umar da Khadija Falalu-Umar mai shekaru 7, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Wasu Fusatattu Mutanen Gari Suka Tari Yan Bindiga, Suka Hallaka Daya Daga Ciki a Taraba

Farar shinkafa babu miya ake bamu sau 1 a rana, Wadanda suka kubuta daga hannun miyagu
Farar shinkafa babu miya ake bamu sau 1 a rana, Wadanda suka kubuta daga hannun miyagu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wanne hali suka shiga yayin da suke hannun miyagu?

Ta bayyana yadda suka fuskanci kalubale iri-iri inda tace:

Basu dauremu ba kamar yadda suke yi wa manya; suna barinmu muyi cudanya da yaransu kafin su tafi kiwon shanu. Suna bamu farar shinkafa ne da mai da dan magi sau daya a rana, watarana kuma basu bamu komai.

Ta yaya suka tsere?

A cewarta sun gudu ne daga hannun masu garkuwa da mutanen a wani dare lokacin ana ruwan sama kuma wanda yake gadinsu yana bacci.

Ta kara da bada labarin yadda suna hanyar guduwa suka hadu da wani wanda ya sato wasu yaran sai ya tambayesu inda zasu je suka ce an sakesu ne aka bar su anan cikin dajin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a cewarta, mutumin ya nace sanin ko guduwa suka yi amma yaran suka tsaya akan magana daya.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

Mutumin ya mayar damu wani wurin inda muka kwana. Washegari ana ruwan sama muka cigaba da tafiya har muka je wani kauyen da yake kusa da taimakon mutumin.
Muna cikin tafiya cikin ruwan saman Bashir ya fadi, sai dai daya daga cikinmu ya dauke shi har sai da muka kai wani wuri inda waya take iya shiga.
Mutumin ya tsaya yace mu tafi can gaba zamu ga mutanen da za su kaimu wani kauye a can gaba.

Tace suna tafiya suka isa wani wuri mai mamakon ruwan sama, dole suka tsaya kafin ruwan ya ragu kafin suka wuce.

A cewar Halima sai da suka wuce ruwan sannan suka hadu da wasu mutanen kirki da suka kaisu har kauyen Sabon Birni.

Yarinyar mai shekaru 10 ta bayyana yadda masu garkuwa da mutanen suke zaune tare da iyalinsu wadanda suke fita kiwo kullum.

Akwai amarya da kawayenta a sansani da yaran suka baro

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Tace a sansanin har da amarya da kawayenta, mace mai shayarwa da mutane da dama wadanda aka daure kamar dabbobi.

Mahaifin yaran, Alhaji Nura Jibrin, shugaban kauyen Dutsen Abba dake karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna ya ce an sace yaran nashi 3 tare da wasu mazauna kauyen guda 4 a ranar 9 ga watan Yuni.

Dagacin kauyen ya sanar da manema labarai a Zaria cewa an saki sauran mutane 4 a ranar 26 ga watan Yuni bayan an biya kudin fansa naira miliyan 3.

An biya kudin fansa amma miyagu sun ki sakin yaran

Jibrin ya sanar da yadda a watan Yuli ana saura kwana kadan babbar sallah masu garkuwa da mutanen suka bukaci a basu N500,000 kuma aka biya su amma suka ki sakin yaran.

Yace a ranar 6 ga watan Augusta suka bukaci sabon babur ko kuma N300,000 don su saki yaran amma ba a basu ba.

Kara karanta wannan

Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

Ina zaman jira ranar 8 ga watan Augusta, kwana 59 da faruwar lamarin aka sanar dani cewa yarana sun gudu daga hannun masu garkuwa da mutane kuma an tura su Sabon Birni, karamar hukumar Igabi.
Wani ya kira ya sanar dani inda zan ga yarana. Bayan nan muka tafi Sabon Birnin muka maido da yaran gida,” a cewar dagacin kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel