Kashi 40% na motocin da ake kawowa Najeriya daga waje na sata ne, Ministar Kudi
- Gwamnatin tarayya ta samar da tsarin rijistar motoci na bai daya
- Ministar gwamnati tace Najeriya ta zama hedkwatar shigo da motocin sata
- Yan Najeriya sun shahara da shigo da motoci daga Kotonou
Abuja - Ministar kudi da kasafin kudi, Hajiya Zainab Ahmed, a ranar Alhamis ta bayyana cewa akalla kashi 40% na motocin da aka shigo da su Najeriya na sata ne.
Hajiya Shamsuna ta bayyana hakan ne a taron wayar da kai kan sabon tsarin rijistan motoci ta kasa watau National Vehicle Registry (VREG) a Abuja, rahoton Tribune.
Tace:
"Cibiyar lissafi a Najeriya NBS ta tabbatar da cewa tsakanin 2015 da 2019, Najeriya ta shigo da akalla motoci 300,000..kuma an samu karin motocin da aka shigo da su ta barauniyar hanya da kashi 45%."
"Wani bincike ya bayyana cewa Najeriya ta zama hedkwatan motocin sata saboda ba'ayi rijistan lambar VIM na motoci ba, kuma ba za'a iya bibiyarsu ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me yasa aka samar da tsarn VREG?
Ministar ta ce sun samar da VREG ne domin kara kudin shigar gwamnati saboda za'a fara amfani da ilimin zamani wajen fadada hanyoyin samar da kudin shiga wa Najeriya da kuma dakile garkuwa da mutane, da kuma amfani da motoci wajen aikata ta'addanci.
VREG wani tsari ne da zai samar da manhajar bai daya da dukkan hukumomin gwamnati zasu amfani wajen sannin sahihin mammalakin mota a Najeriya.
Asali: Legit.ng