Yadda mu ka ga bayan ‘Yan bindiga 123 a ‘Jihar Zamfara a cikin ‘yan kwanaki Inji Dakarun Sojoji

Yadda mu ka ga bayan ‘Yan bindiga 123 a ‘Jihar Zamfara a cikin ‘yan kwanaki Inji Dakarun Sojoji

  • Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga fiye da 100 a jejin Zamfara
  • Jami'in Hedikwatar tsaro ta kasa, Janar Benard Onyeuko ya bayyana haka
  • Su ma Dakarun Operation Whirl Stroke sun damke ‘Yan bindiga a Taraba

DHQ ta fitar da jawabin nasarorin da ta samu

Abuja - A ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021, Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bada sanarwar nasarar da ta samu a kan ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe akalla ‘yan bindiga 123 a Zamfara.

Rundunar Operation Hadarin Daji sun yi raga-raga da mafakar ‘yan bindigan a dajin Dansadau, jejin Kwiambana, dajin Sabubu da kuma yankin Dudufi.

Jaridar Punch tace Darektan rikon kwarya na yada labaran hedikwatar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya bayyana haka da yake jawabi a jiya.

Kara karanta wannan

Labari mara dadi: An tsinci gawar babban Limamin da aka yi garkuwa da shi a cikin mota

Birgediya Janar Benard Onyeuko ya ke cewa an samu wannan nasara ne a makonni biyu da suka wuce.

“Tsakanin 2 zuwa 6 ga watan Agustan 2021, sojojin saman Operation Hadarin Daji sun kai wa ‘yan bindiga hare-hare a inda suka fake a kudancin garin Dansadau, Arewa da jejin Kwiambana, da kuma Arewacin dajin Sububu da kauyukan Dudufi a yankin Faru, karamar hukumar Muradun, duk a jihar Zamfara.”

Shugaban hafsun sojoji
Shugaban hafsun sojojin kasa, Farouk Yahaya Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

“Luguden saman da aka kai ya yi sanadiyyar ruguza gidajen har da wani daga cikin shugaban ‘yan bindigan, Halilu Tubali, yayin da su ke yin wani taro.”
“Hare-haren saman da kuma gudumuwar da sojojin kasa suka bada, ya taimaka wajen ganin bayan ‘yan bindiga 123, tare da rusa masu kayan tafiyarsu.”

Aikin Operation Whirl Stroke ya na kyau

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

Har ila yau, Janar Benard Onyeuko ya ce dakarun Operation Whirl Stroke da ke Taraba sun kama ‘yan bindiga da masu taimaka masu da bayanai a Benuwai da Taraba.

Sojojin sun kuma karbe bindigogin AK-47 shida, da SMG daya, da kananan bindigogi biyu, da casbi 66 na harsashin NATO mai mita 7.62 a hannun miyagun.

Ana yin galaba a kan ‘Yan Boko Haram

Sanarwar ta ce ‘yan ta’adda 27 aka kashe, sannan aka kama wasu 51, yayin da sama da 1, 000 suka mika kansu a yakin da ake yi da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Haka zalika an ji cewa wani ‘Dan Boko Haram da ya yi suna a ta’addanci, Amir Adamu Rugu Rugu, ya ji wuya, ya kai kansa ga rundunar sojoji da ke Gwoza, jihar Borno.

Amir Adamu Rugu Rugu ya dade yana kashe Bayin Allah a jejin Sambisa da tsaunukan Mandara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Najeriya ta yi babban rashi na wani masanin tsaro sakamakon cutar korona

Asali: Legit.ng

Online view pixel