Hatsabibin Mayakin Boko Haram da Sojoji suka ce sun kashe a 2019, ya mika kansa da kansa

Hatsabibin Mayakin Boko Haram da Sojoji suka ce sun kashe a 2019, ya mika kansa da kansa

  • Adamu Rugu Rugu da ‘Ya ‘yansa da mata sun hakura da yaki da sojojin Najeriya
  • Rahotanni sun ce yau Rugu da Iyalinsa suka kai kansu gaban Sojoji dake Gwoza
  • Mutanen Garin Gwoza duk sun san labarin irin ta’adin Amir Adamu Rugu Rugu

Borno - Rahotanni suna nuna cewa wani babban jagoran ‘yan ta’addan Boko Haram, ya mika kansa gaban rundunar sojojin kasa na Najeriya a jihar Borno.

Adamu Hamidu ya ajiye makamai

Jaridar Daily Trust ta ce Amir Adamu Rugu Rugu ya sallama kansa tare da iyalansa ga dakarun Operation Hadin Kai da ke karamar hukumar Gwoza a Borno.

Rahoton yace Adamu Rugu Rugu da yaransa sun yi kaurin-suna sosai wajen ta’addanci a yankin dajin Sambisa da kuma tsaunukan Mandara da ke yankin Gwoza.

Jagoran ‘yan ta’addan ya kan tare matafiya, tare da kai wa jami’an tsaro hari a Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

‘Dan kasuwa ya tsinci kan shi a gidan yari bayan ya sisirfawa Gwamnan jihar Adamawa zagi

Wata majiya daga gidan sojan kasan Najeriya ta tabbatar wa Daily Trust cewa Adamu Rugu Rugu ya mika kansa ne tare da matansa uku da ‘ya ‘yansa a Gwoza.

Wani mazaunin Gwoza ya shaida wa manema labarai cewa mutanen gari sun san wannan ‘dan ta’adda, ya na mai farin cikin kawowar karshen ‘yan ta’addan.

Boko Haram da Sojoji
Sojojin Najeriya a Borno Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

“Mun gode wa Allah, shahararren ‘dan Boko Haram, Amir Adamu Rugu Rugu, ya mika kansa yau a garin Gwoza, Karshen Boko Haram ya zo in Allah ya so.”

Sojoji sun taba cewa sun ga bayan Rugu Rugu

Akwai lokacin da dakarun Operation Lafiya Dole suka bada sanarwar cewa sun kashe Adamu Hamidu, wanda aka fi sani da Adamu Rugu Rugu a farkon 2019.

Jami’in sojan da yake magana da yawun Operation Lafiya Dole a lokacin, Kanal Ado Isa, ya fitar da jawabi, ya na cewa sun ga bayan babban sojan ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Yerwa Express ta ce Rugu Rugu ya shiga Boko Haram ne a 2014, bayan an ci karfin garin Gwoza.

Ya aka yi 'Yan Boko Haram su ke mika wuya?

Sojojin Najeriya sun ce mayakan kungiyar Boko Haram suna ajiye makamansu ne a sakamakon hare-haren da ake yawan kai masu ta sama da kasa a mafakarsu.

Tun a makon da ya gabata ku ka ji cewa sakamakon cigaba da bude wa ‘yan Boko Haram wuta da rundunar sojin Operation Hadin Kai suke yi, sun soma mika wuya.

A makon jiya an samu ‘yan ta’addan Boko Haram da-dama da suka ajiye makamansu, sannan suka mika wuya, cikinsu akwai mayaka 19, da mata 19 da yara 49.

Asali: Legit.ng

Online view pixel