Labari mara dadi: An tsinci gawar babban Limamin da aka yi garkuwa da shi a cikin mota

Labari mara dadi: An tsinci gawar babban Limamin da aka yi garkuwa da shi a cikin mota

Ana zargin cewa ‘Yan bindiga sun kashe Sheikh Mushafau Bakare a jihar Ogun

A jiya aka sace Malamin addinin Musuluncin, a yau da safe aka tsinci gawarsa

Mushafau Bakare shi ne babban Limamin yankin Atiba, ya shahara a Ijebu-Ode

Ogun - Mashahurin malamin addinin musulunci, kuma babban limamin Atiba da ke garin Ijebu-Ode, jihar Ogun, Sheikh Mushafau Bakare, ya rasu.

A jiya aka sace Sheikh Mushafau Bakare

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021, ta ce an samu gawar Sheikh Mushafau Bakare bayan an yi garkuwa da shi.

A ranar Laraba, ‘yanuwa da abokan arziki suka fito suka sanar da cewa an dauke wannan bajimin malami.

Sa’o’i kadan da aukuwar wannan lamari, sai aka samu labarin da ya fi wannan muni, Punch ta ce an samu gawar limamin a cikin wata sabuwar motarsa.

Jami’an tsaro sun gano gawar Malamin a Ikangba

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

Rahotanni sun ce an iske gawar ne a katuwar mota kirar 'Toyota Highlander; a safiyar yau a wajen yankin Ikangba, a karamar hukumar Odogbolu, Ogun.

Mushafau Bakare
Sheikh Mushafau Bakare Hoto: www.cars.com da dailypost.ng
Asali: UGC

Majiya ta shaida wa manema labarai cewa jami’an ‘yan sanda na reshen Obalande, ne suka iske Sheikh Mushafau Bakare ba ya motsi yayin da suke nemansa.

‘Yanuwan babban limamin na garin Atiba, sun yi ta kiran lambar wayarsa a lokacin da ake nemansa ruwa-a-jallo, amma ba a dauki wayar salular ba.

‘Yan jarida sun yi kokarin tuntubar kakakin ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, a game da wannan lamari mai ban takaici, amma ba a iya samunsa ba.

Jaridar The Will Nigeria tace har zuwa yanzu da ake kawo wannan rahoto, ‘yan sandan jihar Ogun ba su fitar da jawabi a game da mutuwar malamin ba.

Ana sa ran an birne shehin malamin da safe a unguwarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

A makon nan ne aka ji labari cewa zagin Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, a fili ya jawo ana shari’a da ‘dan kasuwa, Ali Yakubu Numan a kotu.

Kara karanta wannan

An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola

Ali Numan ya hau dandalin Facebook, ya na kiran Gwamna Ahmadu Umar Fintiri da barawo, kuma uban barayi a Najeriya, hakan ya sa DSS suka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel