Fitacciyar Jarumar a Masana'antar Shirya Fina-Finai, Simela, Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Fitacciyar Jarumar a Masana'antar Shirya Fina-Finai, Simela, Ta Rigamu Gidan Gaskiya

  • Wata fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Mozambique ta rigamu gidan gaskiya
  • Matar mai suna Hermelinda Simela, ta rasu ne yayin da aka kaita asibiti bayan ta samu matsalar haihuwa
  • Abokan aikinta sun yi alhinin mutuwarta, inda suka ce wannan babbar rashi ne a kasar baki ɗaya

Mozambique - Fitacciyar jaruma kuma tauraruwa a masana'antar shirya fina-finan kasar Mozambique, Hermelinda Simela, ta rigamu gidan gaskiya.

Jarumar, wadda tana shirya fina-finai sannan tana bada umarni ta mutu ne sanadiyyar haihuwa a gadon asibiti, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Makusantan jarumar mai shekara 38 a duniya sun kai ta asibiti ne domin kula da lafiyarta bayan ta samu matsala lokacin haihuwa.

Marigayya Hermelinda Simela
Fitacciyar Jarumar Shirya Fina-Finai, Simela Ta Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa jaririyar da marigayya Simela ta haifa tana cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Zamu Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Shekarar 2022, Gwamna Zulum

Ya abokan sana'arta suka ji da mutuwarta?

BBC Hausa ta ruwaito cewa labarin mutuwar jaruma Simela ya yi matukar ɗaga hankulan masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai a ƙasar.

Wani abokin aikinta wanda suka daɗe suna aiki tare, Alvim Cossa, yace ƙasar Mozambique tana jimamin rasa babbar tauraruwa kuma mai bada umarnin.

Cossa yace:

"Hermelinda ta karfafa gwiwar 'yan wasan kwaikwayo sannan ta bayar da dama ga 'yan fim wajen ganin sun yi nasara."

Wace gudummuwa ta bayar a zamaninta?

Rahoto ya nuna cewa Simela ta bada gudummuwa wajen kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo mai muhimmanci a babban birnin ƙasar, Maputo.

Jarumar ta yi nasarar lashe gasar tauraruwar fina-finai a taron Africa Movie Academy Awards bisa rawar da ta taka a wani fim mai suna Virgin Margarida.

Hakazalika, a zamanin rayuwar marigayya Simela ta ziyarci kasashe da dama, waɗanda suka haɗa da Brazil, Netherland, Jamus, India da kuma Spain.

Kara karanta wannan

An Tafka Ruwan Sama a Rana Daya da Ba'a Taba Irinsa Ba Cikin Shekara 100 a Katsina

A wani labarin kuma kun ji cewa Wata Mata Ta Sa Guba a Gabanta Domin Ta Hallaka Mijinta a Kwanciyar Aure

Matar ta yanke hukuncin hallaka mijin nata mai shekaru 43 a duniya ta hanyar sanya masa guba domin ta gaji da zama da shi.

Wata rana ta nemi mijin da su yi mu'amalar aure da shi kuma ya amsa mata, domin shi baisan wainar da ake toyawa ba na kokarin kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262