FCDO: Gwamnatin kasar Ingila za ta batar da Naira Biliyan 8 a kan mutanen jihar Kano
- Birtaniya ta ce za ta kashe Euro miliyan 14 a kan harkar ilimi a jihar Kano
- FCDO mai kula da cigaban kasasshen renon Afrika ce ta bayyana wannan
- Hukumar ta rage tallafin da ta ke ba kasashe a dalilin matsin Coronavirus
Najeriya - Rahotanni suna zuwa cewa Hukumar FCDO mai kula da cigaban kasasshen renon Afrika ta na hasashen kashe Euro miliyan 14.7 a jihar Kano.
Dr. Chris Pycroft ya ziyarci Kano
BBC Hausa ta rahoto cewa Birtaniya ta ce za ta batar da fam miliyan 14 a kan mutanen Kano domin bunkasa ilimi da sauran bangarorin cigaban al’umma.
Rahoton da aka fitar a ranar 12 ga watan Agusta, 2021, ya ce babban jami’in FCDO, Dr. Chris Pycroft, ya bayyana haka da ya kai ziyara zuwa Kano a ranar Laraba.
This Day ta ce Dr. Christopher Pycroft ya yi wani zama na musamman da gwamnatin Abdullahi Ganduje a karkashin yarjejeniyar MAD a gidan gwamnatin Kano.
Christopher Pycroft, shi ne babban darektan da ke kula da cigaban ayyukan FCDO a Najeriya. A lissafin canji a yau, kudin da za a kashe ya Naira Biliyan 8.334.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
FCDO mai kula da cigaba kasashe renon Ingila ta na kokarin inganta sauran bangarorin rayuwa a lokacin da Ingila ta rage tallafin da ta ke ba kasashen Duniya.

Asali: UGC
FCDO ta rage kasafin kudin 2021
Gwamnatin kasar Ingila ta zaftare 29% daga cikin kasafin kudin abin da ta ke tallafa wa kasashen da ta rena, hakan ya sa tallafin ya ragu daga 0.7% zuwa 0.5%.
Darektan na FCDO yace a wannan karo za a maida hankali ne wajen ayyukan cigaba da inganta rayuwar marasa galihu a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.
A maimakon bada gudumuwar tsabar kudi da marasa karfi, FCDO za ta taimaka wajen rage talauci ta hanyar bunkasa sha’anin kiwon lafiya, ilmi da sauransu.
A shekaru bakwai da suka wuce tsakanin 2014 da 2021, FCDO ta kashe fam miliyan £130 a jihar Kano. Daga shekarar bara zuwa bana, hukumar ta kashe £14.7.
Dala ta na murkusa Naira a kasuwa
Ku na da labari cewa a halin yanzu masu sana’ar ‘Bureaux de Change’ sun daina ganin Dala daga CBN bayan an zarge su da taimaka wa masu barna a Najeriya.
Hakan ya jawo karancin Dala wanda hakan ya sa Naira ta komai N515. Bayan Naira ta yi hobbasa a makon da ya wuce, Dalar Amurka ta cigaba da doke ta a yanzu.
Asali: Legit.ng