Jerin ka'idoji 3 da gwamnatin Buhari ta ba Twitter kafin a dage dokar haramtata
- Gwamnatin Buhari ta amince Twitter ya dawo aiki a Najeriya, sannan an ba kamfanin ka'idoji
- Kamfanin ya amince da bukatar gwamnati, ya kuma sanar da cewa zai kafa ofishi a Najeriya
- Najeriya ta lissafo wasu ka'idoji guda 3 da ta ce dole kamfanin ya cika su kafin ya dawo aiki
Bayan dakatar da Twitter a Najeriya, kamfanin da gwamnatin Najeriya sun cimma matsaya.
A cewar Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, wanda ya sabunta bayani ga 'yan Najeriya kan batun, ya ce kamfanin ya amince zai biya wasu bukatun gwamnati, in ji PR News.
Ya ce Twitter ya amince da yin wadannan:
1. Samar da ofishi a Najeriya tare da yin rijista da hukumar harkokin kasuwanci
Ya ce saboda son yin kasuwanci a Najeriya, dole ne su kasance suna da ofishi a cikin kasar. Ya ce saboda haka dole ne su samar da adireshi, The Cable ta kara da cewa.
2. Samar da wakilin Twitter a Najeriya
Mohammed ya kuma ce ya zama dole kamfanin ya dauki wakilan kasar da zai zama wakilin Twittera Najeriya. Ya ce dole ne wakilin ya kasance ma’aikacin Twitter wanda zai iya zama mai sadarwa tsakanin Najeriya da Twitter.
"Mun yi imanin cewa yana da mahimmanci Twitter ya kasance yana da wakilin kamfani wanda ke sama. Domin ya iya kai korafi kai tsaye daga Najeriya zuwa Twitter."
3. Yin rijista da hukumomin da abin ya shafa
Mun kuma umarci Twitter, baya ga yin rijistar kamfanin a Najeriya, dole ne kuma ya yi rajista da hukumomin da suka dace kamar su NIPDA, NCC da hukumar watsa labarai.
Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya
A wani labarin, Gwamnatin tarayya, ta hanyar ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ta sanar da dage dokar hana Twitter, kana kamfanin zai bude ofishinsa a Najeriya.
Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, yayin da yake zantawa da wakilan gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.
Ministan ya ce ya zuwa yanzu, gwamnati ta dage dakatar da shafin tare da wasu sharudda wadanda wasu daga ciki sun hada da yin rijista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC).
Asali: Legit.ng