Tashin Hankali: Wata Mata Ta Sa Guba a Gabanta Domin Ta Hallaka Mijinta a Kwanciyar Aure

Tashin Hankali: Wata Mata Ta Sa Guba a Gabanta Domin Ta Hallaka Mijinta a Kwanciyar Aure

  • Wata mata a kasar Brazil ta yi yunkurin hallaka mai gidanta ta hanyar sanya masa guba
  • Matar ta yi amfani da gabanta, inda ta sanya guba da niyyar kashe mijinta idan ya kusanceta da mu'amalar aure
  • Sai dai mijin bai faɗa wannan tarko ba, inda ya fasa kusantarta bayan yaji wani wari na tashi a gabanta

Brazil - Wata mata yar ƙasa Brazil ta kusa sheke kanta yayin da ta sanya guba a gabanta domin ɗana wa mijinta tarko ta kashe shi wurin kwanciyar aure, kamar yadda aminiya ta ruwaito.

Matar ta yanke hukuncin hallaka mijin nata mai shekaru 43 a duniya ta hanyar sanya masa guba domin ta gaji da zama da shi.

Wata rana ta nemi mijin da su yi mu'amalar aure da shi kuma ya amsa mata, domin shi baisan wainar da ake toyawa ba na kokarin kashe shi.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Yi Wuf da Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Wata Mata ta yi yukurin kashe mijinta a Brazil
Tashin Hankali: Wata Mata Ta Sa Guba a Gabanta Domin Ta Hallaka Mijinta a Kwanciyar Aure Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Ta ya aka gano shirin matar?

Mijin ya bayyana cewa bayan sun gama shirin kwanciyar aure, yana gab da ya kusance ta ne sai yaji wani irin wari na tashi daga al'aurarta.

Aminiya ta ruwaito mutumin na cewa:

"Jin wannan wari ya dakatar dani, inda na umarce ta da taje asibiti dake Unguwar da muke, Sao de Jose Rio Preto."

Bayan likitoci sun yi gwaje-gwajensu ne suka gano cewa an sanya guba a al'aurar matar, wanda zata iya kashe su dukka idan suka yi mu'amalar aure.

Shin matar ta amsa laifinta?

Da matar taji sakamakon gwaje-gwajen da aka mata harma gubar ta fara aiki a jikinta, nan take ta tabbatar musu da duk shirinta na yunkurin kashe maigidanta.

A halin yanzun jami'an yan sandan kasar na cigaba da tsananta bincike game da lamarin yayin da ake jiran sakamakon wasu ragowar gwaji daga likitoci.

Kara karanta wannan

Ba su yarda mata za su iya jagoranci ba, za mu nuna masu kuskurensu: Shugabar Kasar Tanzania ta magantu

Wane mataki mijin ya ɗauka?

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin ya yi matukar fusata da jin shirin matar tasa duk da cewa shine ya matsa mata tazo asibiti.

Mutumin ya sha alwashin kai karar matar gaban alkali domin nema masa hakkinsa na kokarin kashe shi da ta yi.

A wani labarin kuma kun ji Yadda Wasu Fusatattu Mutane Suka Tari Yan Bindiga, Suka Hallaka Daya Daga Ciki a Taraba

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Jauro Manu dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.

Mutanen gari da ɗumbin yawansu suka dakile harin da aka kaiwa wani babban manomi a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel