Magoya bayan Barcelona sun kai kara da nufin haramtawa PSG daukar Lionel Messi

Magoya bayan Barcelona sun kai kara da nufin haramtawa PSG daukar Lionel Messi

  • Dr. Juan Branco ya kai karar kungiyar PSG a kan yunkurin daukar Lionel Messi
  • Ana neman hana ‘dan wasa Messi buga wa PSG saboda dokar Financial Fair Play’
  • Masu karar sun ce duk kudin PSG suna tafiya ne wajen biyan albashin ‘yan wasa

Spain - Jaridar Marca ta kasar Sifen ta rahoto cewa har yanzu da sauran rina a kaba game da makomar tauraron ‘dan wasan Duniya, Lionel Messi.

Rahoton Marca ya bayyana cewa an kai korafi gaban hukumar kwallon kafa ta Turai da nufin a hana kungiyar Paris Saint-Germain sayen Lionel Messi.

PSG za ta saba dokar Financial Fair Play irin Barcelona

Korafin da ake yi shi ne kungiyar kwallon kafan Faransa, PSG za ta saba dokar nan ta ‘Financial Fair Play’ idan ta saye tsohon ‘dan wasan na Barcelona.

Dr. Juan Branco ya shigar da kara a gaban kotu a madadin magoya bayan kungiyar Barcelona.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

Korafin da Branco yake yi shi ne halin tattalin arzikin da PSG ta ke ciki a yau, ya fi na Barcelona da ta gagara ba Messi sabon kwantiragi, tabarbare wa.

"A kakar 2019/20, kashi 99% na kudin-shigan PSG ya tafi ne wajen biyan albashi, yayin da 54% na kudin da Barcelona ta samu ne ta batar kan albashi.”

Lionel Messi
Leo Messi ya na kuka zai bar Barcelona Hoto: Barcelona
Asali: Facebook

Wadanda suka shigar da wannan kara suna sa rai hakan ya sa Messi ya gaza koma wa kasar Faransa, suna cewa kudin PSG zai kare wajen biyan ‘yan wasa.

Kudin da PSG ta ke kashe wa wajen biyan albashi

Cikin hujjojin da aka gabatar a karar akwai batun sababbin cefenen da PSG ta yi; Gianluigi Donnarumma, Sergio Ramos, Achraf Hakimi, da Georginio Wijnaldum.

Baya ga haka, kungiyar PSG ta na kashe makudan kudi duk shekara waje biyan taurarin ‘yan wasanta irinsu Kylian Mbappe, Neymar da kuma Marco Verratti.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

A baya an ji labari cewa 'dan wasan Argentina, Messi zai cigaba da zama a Barcelona har 2027, amma zai rasa Naira Biliyan 20 duk shekara daga cikin albashinsa.

Tauraron ya so a ce ya sabunta kwantiraginsa, ya zauna a Barcelona har zuwa kakar 2027.

Sai dai Barcelona ta gaza ba Messi sabon kwantiragin domin ko da ‘dan wasan ya rage albashinsa da 50%, abin da za a batar, ya zarce kudin da aka ware na albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel