Dawowar Korona karo na 3: Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sake kafa dokar kulle

Dawowar Korona karo na 3: Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sake kafa dokar kulle

  • Gwamnatin tarayya ta ce adadin mutanen da suka kamu da COVID-19 karo na uku bai kai a kafa dokar kulle ba
  • Dr Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai
  • Ministan yace Najeriya ta biya kudin alluran rigakafin J&J guda milyan 30 daga Amurka

Fadar Aso Rock, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce bata shirya kafa wani sabon dokar kulle ba duk da dawowar cutar COVID-19 a fadin tarayya.

Channels TV ta ruwaito cewa ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 12 ga Agusta, a taron mako-mako na hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa Ministan yace adadin mutanen da suka kamu bai kai a kakaba sabuwar dokar kulle ba.

A ranar Laraba, 11 ga Agusta, hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDc ta cewa sabbin mutane 790 suka kamu da cutar Korona.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya

Wannan shine adadi mafi yawa cikin watanni shida.

Wannan sabuwar yaduwar da cutar keyi ya biyo bayan bullar sabuwar launin cutar da aka fi sani da 'Delta'.

Dawowar Korona karo na 3: Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sake kafa dokar kulle
Dawowar Korona karo na 3: Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sake kafa dokar kulle Hoto: NCDC
Asali: UGC

Najeriya ta biya kudin rigakafin COVID-19

Ehanire ya kara da cewa bayan rigakafin da Najeriya ta nema kyauta, Najeriya ta biya kudin kwayoyin rigakafin Johnson&Johnson guda milyan 30.

A cewarsa, tunda farashin allurar ya sauka yanzu, ana sa ranar sayan guda milyan 40.

Ehanire yace tuni rigakafin Johnson&Johnson guda 176,000 sun isa Najeriya yayinda sauran ke hanyar zuwa.

Najeriya ta yi babban rashi na wani masanin tsaro sakamakon cutar korona

A ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, an rasa daya daga cikin fitattun masana harkar tsaro, Cif Ona Ekhomu, wanda ya rubuta littafin, ‘Boko Haram: Security Considerations and the Rise of an Insurgency’.

Ekhomu ya mutu a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, a jihar Legas bayan ya yi fama da cutar COVID-19.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m

Shugaban na Kungiyar Tsaro da Kariya na Masana'antu na Najeriya (AISSON) ya mutu yana da shekaru 66 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel