‘Dan kasuwa ya tsinci kan shi a gidan yari bayan ya sisirfawa Gwamnan jihar Adamawa zagi
- Ana zargin Ali Yakubu Numan da zagin Gwamnan Adamawa a Facebook
- Hakan ya sa aka kai karar wannan mutum wajen DSS, kuma aka cafke shi
- Yanzu magana har ta je gaban kotu, Alkali ya tsare sa a gidan gyaran hali
Adamawa - Wani ‘dan kasuwa mai suna Ali Yakubu Numan, yana tsare a gidan gyaran hali saboda zarginsa da ake yi da zagin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
Me ya jawo wa Ali Numan zuwa kurkuku?
Jaridar Punch ta ce wani Alkalin kotun majistare, Mai shari’a Japhet Ibrahim Basani, ya bada umarnin garkame ‘dan kasuwan a dalilin cin mutuncin gwamna.
Ali Yakubu Numan ya caccaki Mai girma Ahmadu Umaru Fintiri a shafinsa na Facebook a ranakun 11, 12, 13, 17, 20, da na 29 na watan Yulin shekarar 2021.
The Guardian ta ce wannan mutum ya kira gwamnan na jihar Adamawa da "barawo, uban barayin Najeriya.”
Rahoton ya ce Ali Numan ya fito fili yana zargin gwamnan da cewa ya saci taliya, sannan ya wawuri biliyoyin kudin al’umma, ba tare da ya kawo hujjoji ba.
Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, ya kai korafi ta hannun lauyansa, M. A. Adamu a wani kotun majistare.
M. A. Adamu ya fada wa kotu cewa abin da wannan mutumi ya yi, zai iya jawo hayaniya daga wajen magoya bayan gwamna, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri.
Lauyan yace wani jagoran matasa na jam’iyyar PDP a Yola, ya kai karar Ali Numan wajen jami’an DSS, kuma tuni hukumar ta yi ram da shi domin a hukunta shi.
Bayan an saurari korafin da gwamnati ta gabatar, lauyan na ta ya bukaci Alkali Japhet Ibrahim Basani, ya ba shi lokaci ya kawo wanda ake tuhuma a gaban kotu.
Mai shari’a Japhet Ibrahim Basani ya amince da wannan roko, ya bukaci a cigaba da tsare Numan a gidan maza har zuwa lokacin da za a cigaba da sauraron shari’ar.
Ana zargin Chinaza Okoh da satar jariri
Rahotanni sun ce ana zargin wata mata mai suna Chinaza Okoh da laifin sace karamar yarinyar 'yaruwarta, ta saida wa wasu mutane biyu a garin Mmaku, Enugu.
Sai dai kuma ‘yan Sanda sun ce sai an kawo kudi sannan za su binciko inda aka kai yarinyar.
Asali: Legit.ng