Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lissafo abubuwan dake rura wutan rashin tsaro a Najeriya

Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lissafo abubuwan dake rura wutan rashin tsaro a Najeriya

  • Shugaban hukumar yaki da rashawa a Najeriya ICPC ya ce gurbacewar tattalin arziki da kuma rashawa da ta'annati ne manyan abubuwan da ke ruruta matsalar tsaro a Najeriya.
  • Bolaji Owasanoye a jawabin da ya saki yace idan ba'a sanya ainun nazari kan alakar dake tsakanin rashawa da rashin tsaro ba, za'a samu matsala.
  • Shugaban na ICPC ya kara da cewa akwai bukatar hada kai da hukumar NSCDC saboda kawo gyara a Najeriya.

Abuja - Shugaban hukumar yaki da rashawa da ta'annati watau ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce abinda ya haddasa matsalar tsaro a kasar shine cin hanci da rashawa da kuma gurbacewar tattalin arziki.

DailyNigerian ta ruwaito cewa kakakin ICPC , Azuka Ogugua, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba, 11 ga Agusta, a Abuja cewa Shugaban na ICPC ya yi wannan magana ne yayinda ya karbi bakuncin kwamandan NSCDC, Ahmed Audi.

Owasanoye ya kara da cewa hadin kan wadannan hukumomin gwamnati biyu na da muhimmanci don kawo gyara kasa da kuma samun labaran leken asiri domin yaki da rashawa.

The Guardian ta ruwaito cewa kwamandan NSCDC Audi ya bukaci taimakon ICPC wajen horar da jami'an hukumarsa kan yadda ake tattara labaran leken asiri da kuma bincike.

Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lissafo abubuwan da rura wutan rashin tsaro a Najeriya
Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lissafo abubuwan da rura wutan rashin tsaro a Najeriya Hoto:ChannelsTV
Asali: UGC

Sojoji sun cafke mutum 8 da ake zargi da hannu a bindige mata 3 a Bassa, Filato

A bangare guda, rundunar Operation Safe Heaven a ranar Talata, 10 ga watan Augustan 2021 ta kama mutane 8 da ake zargin suna da hannu a harbin wasu mata 3 a wata gona dake kusa da Rafin Bauna dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Rundunar ta amsa kiran gaggawar da aka yi mata akan kisan mata 3 da suke kusa da Rafin Bauna wadanda wasu ‘yan bindiga suka harbe.

Take anan rundunar tayi gaggawar isa wurin inda ta riski mata 3 cikinsu har 2 sun mutu daya kuma rai a hannun Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel