Ba za'a iya hada kai a APC ba, masu dogon buri sun mamaye jam'iyyar, sun shake mata wuya: Solomon Dalung

Ba za'a iya hada kai a APC ba, masu dogon buri sun mamaye jam'iyyar, sun shake mata wuya: Solomon Dalung

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya koka da yadda masu son zuciya suka cika jam'iyyar APC
  • Fitaccen dan siyasan kuma dan asalin jihar Filato yace babu shakka miyagu sun shake jam'iyyar kuma ba zasu saketa
  • A cewarsa, wadanda suka rike jam'iyyar duk da sun san halin da ta shiga suna da dogon buri kuma ba ta 'yan kasa suke ba

Jos, Filato - Legit.ng ta zanta da tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung. Fitaccen dan siyasan ya zanta da Legit.ng ne kan rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar APC.

Sanannen abu ne cewa ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami SAN ya bada umarnin a yi zabukan shugabannin jam'iyya inda yace babu matsala.

Ba za'a iya hada kai a APC ba, masu dogon buri sun mamaye jam'iyyar, sun shake mata wuya: Solomon Dalung
Ba za'a iya hada kai a APC ba, masu dogon buri sun mamaye jam'iyyar, sun shake mata wuya: Solomon Dalung. Hoto daga Vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Jihar tsohon ministan tana daga cikin jihohin da suka yi zabukan shugabannin jam'iyya a ranar Asabar da ta gabata.

Wanne mataki jam'iyyar APC ke dauka domin hadin kai?

Legit.ng tayi magana kan maslaha da kuma wanne mataki ne jam'iyyar take dauka domin ganin hadin kan 'ya'yan jam'iyyar, Dalung ya koka da yadda masu son mulki da son zuciya suka cika jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar

Ya kara da bayyana cewa babu shakka ba za a iya samun hadin kai a jam'iyyar ba duk da tun farko sun kafa ne domin adalci kuma cike da adalci.

A cewar tsohon ministan, miyagu sun riga sun shiga jam'iyyar kuma sun shaketa tare da kokarin kaita kasa duk da kuwa sun san cewa suna yin abinda bai dace ba.

Ba za a iya ba, domin lokacin da muka kafa wannan jam'iyyar mun kafa ta a kan adalci ne tare da niyyar zamu yi wa 'yan Najeriya adalci kuma domin mu canza yadda ake gudanar da al'amari na gwamnati a Najeriya.
Amma a yanzu, a halin da ake ciki, masu dogon buri na rike damadafun iko bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, sune wadanda suka shakewa jam'iyyar wuya, sun saka guiwa a wuyan jam'iyya duk da kukan da suka ji tana yi na cewa ba zata iya numfashi.

Kara karanta wannan

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

Saboda haka, masu wannan dogon burin babu yadda za a yi su bar jam'iyya ta bi alkiblar da ta aka kafa ta a kai, illa iyaka ta bi abinda ransu yake so da son zuciya koda kuwa 'yan Najeriya suna kuka.

Mafarauta: 'Manyan dabbobi' irin 'yan bindiga da masu satar mutane zamu saka gaba

Kungiyar mafarautan Najeriya ta ce ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane 'manyan dabbobi ne' da yanzu haka suke kokarin farauta a kasar nan.

A ranar Talata a Abuja, kwamanda janar na kungiyar, Joshua Osatimehin yayin tattaunawa da NAN, ya bukaci majalisar tarayya ta sanya hannu akan amincewa da kungiyarsu.

TheCable ta ruwaito cewa, a cewar Osatimehin, matsawar aka sanya hannu akan dokar kuma ta fara aiki, zasu yi iyakar kokarinsu na ganin sun wanzar da tsaro a kowanne lungu da sako dake kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel