Mafarauta: 'Manyan dabbobi' irin 'yan bindiga da masu satar mutane zamu saka gaba
- Kungiyar mafarauta ta Najeriya ta ce ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane 'manyan dabbobi ne' wadanda yanzu haka suke harin kamawa a dazukan kasar nan
- Kwamanda janar na kungiyar, Joshua Osatimehin, a ranar Talata a Abuja ya bayyana takarda wacce ya bukaci majalisar tarayya ta amince da kungiyar ta fara aiki
- A cewar Osatimehin, matsawar aka amince da wannan shirin, kungiyar za ta tabbatar da tsaro a kowanne lungu da sako dake kasar nan
FCT, Abuja - Kungiyar mafarautan Najeriya ta ce ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane 'manyan dabbobi ne' da yanzu haka suke kokarin farauta a kasar nan.
A ranar Talata a Abuja, kwamanda janar na kungiyar, Joshua Osatimehin yayin tattaunawa da NAN, ya bukaci majalisar tarayya ta sanya hannu akan amincewa da kungiyarsu.
Osatimehin ya bukaci gwamnati ta basu dama
TheCable ta ruwaito cewa, a cewar Osatimehin, matsawar aka sanya hannu akan dokar kuma ta fara aiki, zasu yi iyakar kokarinsu na ganin sun wanzar da tsaro a kowanne lungu da sako dake kasar nan.
Akwai sabon salon harkar farauta; yanzu manyan dabbobi muke farauta wadanda sune ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu manyan laifuka da suke cin karensu babu babbaka a dazuka, a cewarsa.
Sanata Olujimi Abiodun na Ekiti ne ya dauki nauyin takardar kuma ya gabatar ga NASS a 2020, kuma ta wuce matakin farko da na biyu a majalisar wakilai data jiha.
An shirya hakan ne don tabbatar da kokarin samar da tsaro a dazuka da lungunan dake cikin kasar nan.
Munad a rassa a Abuja, da sauran jihohi 36 dake fadin kasar nan, sannan mafi yawansu matasa ne, NHC tana aikine kamar jami’an tsaro.”
Mafarauta suna ganin miyagu, amma ba a basu damar maganinsu ba
A cewar kwamanda janar din, mafarauta suna ganin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a dazuka amma basu da damar da zasu kama su, Thecable ta wallafa.
Idan muka shiga dazuka muna ganin miyagun mutane amma bamuda lasisin kamasu, a cewar Osatimehin.
Amma idan za a amince damu a matsayin doka bamuda damar kama wani mai laifi.
Amma idan gwamnati ta amince da lamarinmu kuma gwamnati ta karbi kungiyarmu, tabbas masu laifi zasu ragu a kasar nan.”
PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren 'yan bindiga a jiharsa, TheCable ta wallafa.
A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jihar na fuskantar harin 'yan bindiga a kullum.
A yayin martani ga zancensa, a ranar Lahadi, Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, yace ya dace Masari ya fito fili ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC cewa gwamnatin tarayya ta gaza.
Asali: Legit.ng