Dalilin da ya sa Najeriya ba za ta daina karbo bashi ba - Ministar Kudi

Dalilin da ya sa Najeriya ba za ta daina karbo bashi ba - Ministar Kudi

A yayin da ake ci gaba da korafe-korafe da bayyana damuwa kan nauyin bashin da ya yi wa Najeriya katutu, gwamnatin tarayya ta yi magana kan larurorin da suke tilasta mata cin bashi.

Mun samu cewa, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed, ta bayyana dalilin da ya sa kasar nan ba za ta daina ciwo bashin ba a yanzu.

Ministar ta ce a hakinanin gaskiya, annobar korona da kuma karyewar da farashin man fetur ya yi a kasuwar duniya, su ne dalilai biyu da suke tilastawa kasar nan fita neman bashi a ketare.

Ta bayyana cewa, tun gabanin bullar annobar korona wadda ta janyo karayar tattalin arziki a fadin duniya, Najeriya ta yi fama da karancin kudaden shiga lamarin da ya jefa kasar cikin mawuyancin hali.

Ministar ta zayyana cewa, wannan babban kalubale ya taka rawar gani wajen hana gwamnatin sauke wasu nauye-nauye da suka rataya wuyanta na hidimtawa al'umma.

Furucin ministar ya zo kwanan nan a wani taro ta hanyar gizo da ta halarta tare da wasu kungiyoyin daban-daban masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki da saka hannun jari.

Ministar wacce mai ba wa shugaban kasa shawarwari na musamman kan harkokin kudi da tattalin azriki,Mrs Sarah Alade ta ce gwamnati ta na iya bakin kokarin ta don ganin ta fadada hanyoyin samar da kudaden shiga da kuma rage kashe kudi.

Ministar Kudi; kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed
Hoto daga; Businessday
Ministar Kudi; kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed Hoto daga; Businessday
Asali: Twitter

Ta lura cewa, idan har 'yan kasa suka dage wajen biyan haraji da kuma yin abubuwan da suka dace, zai yi matukar tasiri wajen magance matsalolin kasar, musamman batun samar da kudaden shiga.

Legit.ng ta ruwaito cewa, jimillar bashin kudin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 28.63 (N28.63tn), ofishin kula da basussukan Najeriya DMO ta alanta ranar Alhamis.

A rahoton basussukan kasar da aka saki a daren Alhamis, ofishin DMO ya yi bayanin cewa jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga N27.4tn a Disamban 2019 zuwa N28.63tn a Maris 2020.

KARANTA KUMA: Muna samun nasara a fagen yaki da cutar korona - Ganduje

Hakan ya nuna cewa cikin watanni uku, bashin da Najeriya ta ci ya karu da Naira tiriliyan 1.23.

A yayin da Naira tiriliyan 9.99 daga ciki bashin da an karbo su ne daga kasashen waje, Naira tiriliyan 18.64 kuma an karbo ne daga hannun bankunan cikin gida.

Rahoton da ofishin DMO ya kara nuna cewa Najeriya ta kashe naira biliyan 609.13 wajen biyan wani bangare na basussukan tsakanin watan Junairu zuwa Maris na 2020.

Lissafin wata-wata ya nuna cewa an biya Naira biliyan 251.35 a watan Junairu, naira biliyan 158.12 a Fabrairu, sai kuma naira biliyan 199.658 a watan Maris.

A cikin wadannan watanni uku, gwamnatin tarayya ta samu kudin shiga na Naira biliyan 950.56 sai dai ta yi amfani naira biliyan 943.12 wajen biyan bashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel