Matawalle: Manyan jiga-jigan APC sun cigaba da rigima duk da an yi sulhu a jihar Zamfara
- Ahmed Sani Yarima-Bakura ya ce dole ‘Yan APC su sabunta rajistarsu a Zamfara
- ‘Yan bangaren Abdulaziz Yari, Lawal Liman sun maida wa Yarima-Bakura raddi
- Shugaban APC na rikon-kwarya a jihar Zamfara yace babu dalilin sake yin rajista
Zamfara - Wasu kalamai da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yarima-Bakura ya yi, sun jawo surutu a jam’iyyar APC na reshen jihar Zamfara.
A wata hira da aka yi da Sanata Ahmed Sani Yarima-Bakura, Punch ta rahoto shi ya na cewa duk ‘dan jam’iyya da bai yi rajista ba, ba zai samu kujera ba.
Da yake magana a garin Gusau a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, Ahmed Yarima-Bakura ya ce babu wanda zai yi takara a APC sai wanda ya sabunta rajista.
Tsohon Sanatan ya ce wadanda suka kaurace wa rajista ba za su iya rike mukami a APC nan gaba ba. Amma bangaren Abdulaziz Yari sun yi masa martani.
“Duk wani ‘dan APC da ya ki yin rajista a dalilin sauya-shekar gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC, ba zai yi zabe ba, kuma ba za a zabe shi ba.”
Kalaman Yarima ba su da tushe a tsarin mulki - Liman
Shugaban rikon kwarya na APC a jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman, ya maida martani a ranar Litinin, ya yi watsi da abin da tsohon gwamnan ya ke fada.
Alhaji Lawal Liman ya zauna da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC da ke garin Gusau, ya na cewa maganar Yarima-Bakura ta saba wa dokokin APC.
“Ina so in jawo hankalin jama’a, musamman ‘ya ‘yan jam’iyyarmu a kan wasu kalamai na tsohon Sanata Yarima da su ke yawo a kafafen yada labarai.”
“Yarima ya yi ikirarin cewa nan gaba duk wanda bai sabunta rajistarsa a jam’iyya tare da sababbin shigo wa APC, ba za a dauke shi a matsayin ‘dan jam’iyya ba, saboda haka ba zai iya fito wa takara ko ya shiga zaben shugabannin jam’iyya ba.”
Shin me dokar jam'iyyar APC ta ce?
Shugaban rikon kwaryan ya ce ya kamata Yarima ya san APC ta yi wa mutanen 770, 000 rajista, don haka babu dalilin sake yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar sabon rajista.
Lawal Liman ya yi wa Yarima raddi, yana cewa babu abin da zai iya soke rajista sai mutuwa, murabus, sauya-sheka, karbar mukami a gwamnatin adawa ko kora.
A yau aka ji labari shugaban kungiyar Yarbawa ta YWG ya ce ya kamata mutanen Arewa su fito su goyi-bayan jagoran APC, Bola Tinubu a zabe mai zuwa na 2023.
Kungiyar YWG ta ce za a samu rashin yadda tsakanin Kudu da Arewa idan jam'iyyar APC mai mulki da shugaba Muhammadu Buhari suka yi wa Tinubu butulci.
Asali: Legit.ng