Siyasa: ‘Dan Majalisan APC ya yi watsi da Jam’iyyar da ta ba shi nasara a zaben 2019 a Adamawa

Siyasa: ‘Dan Majalisan APC ya yi watsi da Jam’iyyar da ta ba shi nasara a zaben 2019 a Adamawa

  • ‘Dan Majalisar Mubi ta Kudu, Hon. Musa Umar ya tsere daga jam’iyyar APC
  • Musa Umar ya yi kukan ba ayi da shi a APC, don haka ne ya shiga jirgin PDP
  • Jam’iyyar APC ta ce dama ta ga take-taken ‘Dan Majalisar zai sauya-shekar

Adamawa - Daya daga cikin ‘yan majalisar dokoki na Adamawa, Honarabul Musa Umar, ya sauya-sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP mai mulkin jihar.

Jaridar Daily Post ta ce Musa Umar ya tsere daga jam’iyyar da ta ba shi tikiti, har ya lashe kujerar ‘dan majalisa mai wakiltar Mubi ta kudu a zaben 2019.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, wannan mataki da Honarabul Umar ya dauka, ya kara wa jam’iyyar PDP rinjaye a majalisar dokokin jihar Adamawa.

A halin yanzu APC mai adawa a jihar Adamawa ta na da ‘yan majalisar dokoki 11, yayin da jam’iyyar PDP mai rinjaye ta ke da kujerun majalisa 14 a jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya yi muni yayin da aka nemi shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya yi murabus

Masu fashin baki suna ganin Umar wanda aka fi sani da Bororo ya na harin Sanata ne a majalisar dattawa a zabe mai zuwa a karkashin jam’iyyarsa ta PDP.

Punch ta ce Bororo wanda ya rike kujerar mai ba gwamna shawara wajen harkar jin dadi a lokacin tsohon gwamna Jibrilla Bindow bai jin dadin APC.

Hon. Musa Umar
'Dan Majalisar Adamawa, Hon. Musa Umar Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jaridar ta ce ‘dan majalisar ya fice daga APC ne bayan zargin da yake yi na cewa an maida shi saniyar ware a zabukan mazabun da jam’yyar adawar ta shirya.

“Na gaji da rashin adalcin da ake yi a gidan APC. Ana ta ware ni a duk abubuwan da ake yi. Na tafi, na koma jam’iyyar PDP domin in samu mafita.”

‘Dan siyasar ya na sa rai za a rika dama wa da shi a gwamnatin mai girma, Rt. Hon. Ahmadu Fintiri.

Da jam’iyyar APC ta ke martani a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, 2021, ta ce ta dade da sanin ‘dan majalisar na kudancin Mubi ya kama hanyar sauya-sheka.

Kara karanta wannan

Rigimar cikin gidan PDP ta kara cabewa, wasu shugabanni na barazanar murabus kwanan nan

Alhaji Mohammed Mayas ya ce tun ba yau ba, kafar Umar ta bar PDP, sam ba su yi mamakin jin cewa ya koma PDP ba. Mayasa yake cewa sauya-shekar, ko a jikinsu.

Majalisar dattawa ta bayyana cewa ba ta bada shawarar gwamnati ta kara wasu Jihohi a Najeriya ba. Kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru ya bayyana haka.

‘Yan Majalisa sun ce akwai wasu ka’idojin da ake bi kafin a kai ga kirkirar Jiha a tsarin mulkin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel