Da aka je aka dawo, BOT ta ceci Shugaban PDP daga yunkurin tsige shi, a nada rikon kwarya

Da aka je aka dawo, BOT ta ceci Shugaban PDP daga yunkurin tsige shi, a nada rikon kwarya

  • Majalisar BOT ta yi zama na musamman a kan abubuwan da ke faruwa a PDP
  • Sanata Walid Jibrin ya jagoranci zaman da aka yi, inda aka ceci Uche Secondus
  • Dattawan PDP sun ce babu maganar a ruguza NWC da nadin shugabannin riko

Abuja - Majalisar amintattu na jam’iyyar PDP sun ki goyon bayan kiran da ake yi na tsige majalisar NWC da Prince Uche Secondus ya ke jagoranta.

Ba za a tsige majalisar Prince Uche Secondus ba

Punch ta ce a zaman da aka yi ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, BOT ba ta yi na’am da yunkurin da ake yi na nada wasu shugabannin rikon kwarya a PDP ba.

Sanata Walid Jibrin da sauran ‘yan majalisarsa, sun bukaci a bar Prince Uche Secondus su kammala wa’adinsu, wanda zai kare nan da wasu watanni.

Dattawan jam’iyyar adawar, sun yi tir da wasu kalamai da manyan PDP irinsu Nyesom Wike su ka yi. Wata majiya ta ce an ba NWC kariya a wannan taro.

Kara karanta wannan

Bakare: Abokin tafiyar Buhari ya ba shi shawarar abin yi, ya daina sukar shugabannin baya

“Mun soki kalaman da wani jagora, wanda ya na nan ya yi. Kiran shugabanninmu da ‘'yan tatsar haraji’ da ‘makaryata’, cin mutunci ne, don haka mu ka ce ina!”

Da yake magana da ‘yan jarida bayan zaman, Sanata David Mark ya ce za a kafa wani kwamiti da zai duba koken da ake yi, ya ce za su shawo kan matsalolin.

PDP BOT
Manyan PDP a taron BOT Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

David Mark ya bayyana cewa mai girma gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya halarci zaman da aka yi ne a matsayinsa na daya daga cikin ‘yan majalisar ta BOT.

Har ila yau BOT ta wanke da sauran shugabannin da ke jan ragamar jam’iyyar. Haka zalika an bukaci wadanda suka yi murabus, su koma kan mukamansu.

Da yake jawabi, Uche Secondus ya bayyana cewa sauke ‘yan majalisar NWC daga mukamansu kafin ayi zabe ya na da illa, ya ce hakan zai nakasa jam’iyyar.

Wadanda suka halarci taron BOT a Abuja

Kara karanta wannan

Yunkurin korar Secondus da sauran Shugabannin PDP ya sa Gwamnoni sun rabu zuwa gida uku

Ragowar wadanda suka halarci taron sune; Gwamna Nyesom Wike, da tsofaffin shugabannin majalisa; Abubakar Bukola Saraki, David Mark da Adolphus Wabara.

Akwai tsofaffin gwamnoni; Ahmed Makarfi, Babangida Aliyu, Ibrahim Shema, Liyel Imoke, Olagunsoye Oyinlola, da su Tanimu Turaki, Tom Ikimi da Olisa Metuh.

Jaridar Daily Trust ta ce an ga ‘yan NWC irinsu Umar Ibrahim Tsauri Sanata Suleiman Nazif a taron.

BOT ta yi wa tufkar hanci ne a lokacin da ragowar wasu ‘yan majalisar NWC su ke barazanar barin mukamansu a Jam’iyyar PDP idan ba a yi waje da Secondus ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel