2023: Idan APC, Buhari, suka yaudari Tinubu, jam’iyyar za ta watse inji Kungiyar Yarbawa
- Kungiyar Yarbawa ta ce bai dace Buhari ya yarda ya yaudari Bola Tinubu ba
- Yoruba Welfare Group tayi kira ga APC da Yankin Arewa su bada goyon-baya
- Adegoke Alawuje yace Tinubu ya bada gudumuwa wajen hawan Buhari mulki
Legas- Kungiyar Yarbawa ta Yoruba Welfare Group, ta gargadi shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC a kan cin amanar Asiwaju Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya cancanci a mara masa baya
Daily Trust ta rahoto kungiyar Yoruba Welfare Group, YWG ta na cewa bai dace a tunzura APC mai mulki da shugaban kasa su yaudari jigon jam’iyyar ba.
Shugaban YWG na kasa, Kwamred Adegoke Alawuje ya fada wa ‘yan jarida yayin da aka tattauna da shi cewa ka da a sake a juya baya ga tsohon gwamnan.
A cewar Kwamred Adegoke Alawuje, Asiwaju Bola Tinubu ya bada gudumuwa sosai domin Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC su dare kan mulki.
Ganin irin fadi-tashi da gwagwarmayar da ‘dan siyasar ya yi a tafiyar APC, shiyasa Adegoke Alawuje yake ganin ya kamata a saka masa a zaben 2023.
Akwai bukatar Arewa su yi Bola Tinubu a 2023
Kungiyar YWG ta ce yunkurin yi wa tsohon gwamnan na jihar Legas butulci, zai kara jawo rashin yaddar da ke tsakanin yankin kudu da kuma bangaren Arewa.
Alawuje ya ce idan har APC ta hana Bola Tinubu kai labari a zabe mai zuwa, burin masu kabilanci da ke gargadin ‘dan siyasar kan hada-kai da Arewa zai tabbata.
Baya ga Mai girma shugaban kasa da APC, haka zalika Alawuje ya yi kira ga mutanen yankin Arewa duk su mara wa Asiwaju Tinubu baya fiye da kowa.
Shugaban kungiyar kabilan Yarbawa ya ce Tinubu ya jawo wa kansa makiya a siyasa saboda ya goyi bayan Muhammadu Buhari a zabukan 2015 da 2019.
“Abin da ya sa wasu suke kokari dare da rana domin kai Bola Tinubu kasa shi ne bayan taimaka wa jam’iyyar APC a 2015, ya kuma yi Buhari a zaben 2019.”
“Duk da rashin adalci da watsi da shi da jam’iyya da fadar shugaban kasa ta yi a wancan lokaci.”
Kwamred Alawuje ya ce babban ‘dan siyasar ya na da mabiya a ko ina a fadin kasar nan, don haka hana shi neman mulki zai jawo wa jam’iyyar APC ta wargaje.
Shugaban muryar Nigeria, VON, kuma babba a APC, Osita Okechukwu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai yi alkawarin mika mulki ga Bola Tinubu ba.
Hakan na zuwa ne bayan irinsu Rufai Hanga sun ce akwai yarjejeniyar da ke nuni da cewa Buhari zai mika ragamar mulkin Najeriya ga Tinubu idan ya gama wa'adinsa.
Asali: Legit.ng