Kocin Real Madrid ya bi Cristiano Ronaldo zuwa Kungiyar Juventus

Kocin Real Madrid ya bi Cristiano Ronaldo zuwa Kungiyar Juventus

Mun samu labari cewa tsohon mai horas da ‘Yan wasan Kungiyar kwallon kafa na Real Madrid watau Zinedine Zidane za su hade da tsohon ‘Dan wasan sa Cristiano Ronaldo a Kungiyar Juventus.

Kocin Real Madrid ya bi Cristiano Ronaldo zuwa Kungiyar Juventus
Juventus ta dauko Zidane bayan Ronaldo domin yin zarra a Turai

A karshen kakar bana ne Kocin Real Madrid ya ba kowa mamaki inda ya sanar da cewa zai tashi daga Kungiyar. Hakan ya zo ne jim kadan bayan an buga wasan Gasar Zakarun Turai inda Real Madrid ta kafa tarihi a Duniya bayan doke Liverpool.

Ana tsakiyar buga Gasar cin kofin Duniya ne kuma aka ji kwatsam babban ‘Dan wasan Duniya Ronaldo zai bar Real Madrid. ‘Dan wasan gaban da ake ji da shi ya tattara ya koma Juventus ne bayan yayi shekaru 9 a Kungiyar Real da ke Sifen.

KU KARANTA: Lokacin da Real tace ba za ta rabu da Ronaldo ba

Yanzu labari ya zo mana cewa tsohon Kocin na Madrid da babban ‘Dan kwallon na kasar Portugal za su hadu a Kasar Italiyan a karshen shekarar nan. Zidane ya samu aiki ne da Juventus a matsayin babban Darekta karkashin tsohon Kulob din sa.

Zidane zai yi aiki ne da Kocin Juventus Max Allegri domin ganin Kungiyar ta lashe Gasar Nahiyar Turai na shekara mai zuwa. A shekarun baya Juventus ta kai har wasan karshe amma ta sha kashi hannun Zidane a Real Madrid da kuma Barcelona.

Tsohon ‘Dan kwallon na Juventus ya ci wa Real Madrid kofin Champiosn league har sau 3 a jere kafin ya bar kulob din. ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo yana cikin kashin-bayan nasarorin da aka samu inda ya ci kwallaye 450 a zaman sa a kulob din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Online view pixel