Alkali ta tsare ‘Dan cikin Marigayi Ummaru ‘Yar’adua a gidan yari bisa zargin kashe mutum 4

Alkali ta tsare ‘Dan cikin Marigayi Ummaru ‘Yar’adua a gidan yari bisa zargin kashe mutum 4

  • Wani ‘Dan Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’adua ya buge mutane 6 a hadarin mota
  • ‘Yan Sanda sun ce Aminu ‘Yar’Adua ya kashe mutum hudu wajen tukin ganganci
  • Kotu ta ce a tsare ‘Yar’Adua a kukurku, za a koma kotu ranar 19 ga watan Agusta

Adamawa - A ranar Alhamis, kotun majistare da ke zama a garin Yola, jihar Adamawa, ta tsare ‘dan tsohon shugaban Najeriya, Aminu Yar’Adua, a gidan yari.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Alkali ya bukaci a rike Aminu Yar’Adua mai shekara 36 ne saboda zarginsa da laifin kashe wasu mutane hudu a Yola.

PM News ta ce dalibin na jami’ar Amurka da ke Najeriya watau AUN, ya jawo wani mummunan hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Bayin Allah kwanaki.

Ana zargin cewa gangancinsa ne ya kai ga faruwar wannan hadari a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, 2021.

Aminu Yar’Adua ya na gudun hauka a hanya - FIR

Binciken ‘yan sanda na FIR da aka gabatar a kotu ta hannun wani jami’i, Zakka Musa, ya na tuhumar Aminu Yar’Adua da buge mutane shida a babban titin Yola.

Zakka Musa ya shaida wa kotu cewa Aminu Yar’Adua ya na tuki ne a guje, wanda hakan ya jawo ya buge wadannan mutane shida, wadanda hudu sun mutu tun tuni.

Marigayi Ummaru ‘Yar’adua
Marigayi shugaba 'Yar'adua

Ragowar mutane biyun da Allah ya yi wa gyadar doguwa, sun samu rauni. Dukkaninsu mutanen garin Sabon Pegi ne a karamar hukumar Yola ta kudu, Adamawa.

Masu hakkin jini sun ce a biya su diyyar N15m

“Wanda suka mutu a hadarin su ne; Aisha Umar (30), Aisha Mamadu (32), Suleiman Abubakar (2) and Jummai Abubakar (30)."
"Sai kuma Rejoice Annu (28) and Hajara Aliyu (27) da sun samu rauni.”

Jami’in da ya ke karar ‘Yar’adua ya shaida wa kotu cewa ‘yan uwan Aisha Umar, Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar suna neman N15m a matsayin diyya.

‘Yar’adua ya musanya ikirarin da ‘yan sanda su ka yi, a karshe Alkali Jummai Ibrahim ta bukaci a tsare shi a kurkukun Yola, za a cigaba da shari’a nan da makonni biyu.

A baya kun samu rahoto daga mujallar FORBES cewa an fitar da jerin kasurguman Attajirai da suka fito daga Najeriya, da adadin kudinsu da kuma silar dukiyarsu.

Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu da kuma Mike Adenuga ne su ka fi kowa kudi a Najeriya. Wadannan manyan Attajirai sun mallaki Naira Tiriliyan 10 a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel