Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga Ta Sama da Kasa a Kaduna, Sun Kashe Sanannun Yan Ta'addan
- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da nasarar sojojin sama da na kasa a wani hari da suka kai maɓoyar yan bindiga
- Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa dakarun soji sun hallaka sanannun yan ta'adda 4 tare da wasu da yawa
- Gwamna Malam Nasiru na jihar ya nuna tsantsar farin cikinsa da wannan nasarar ta sojoji
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna, ranar Lahadi tace sojoji sun kashe manyan sanannun yan bindiga huɗu a maɓoyarsu da aka fi sani da Maikwandaraso dake yankin karamar hukumar Igabi.
Dailytrust ta ruwaito cewa an kashe sanannun yan ta'addan ne a harin sama da dakarun sojin suka kai maɓoyarsu.
Wannan na cikin harin haɗin guiwa da jami'an sojin ƙasa da na sama suka shirya kaiwa maɓoyar yan bindigan dake yankin.
Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya jero sunayen yan bindigan da aka kashe waɗanda suka haɗa da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo da Sulele Bala.
Yan Bindiga nawa sojojin suka kashe?
Kwamishinan ya cigaba da cewa yan bindiga da yawan gaske sun hallaka a yayin harin ta sama da kuma ƙasa.
Wani sashin jawabin yace:
"Yayin da gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i ya samu rahoton wannan nasara ya nuna jin daɗinsa da gamsuwarsa bisa namijin kokarin da sojoji ke yi na kawo karshen yan bindiga a jihar."
Gwamna ya yabawa sojojin da suka jagoranci harin
Gwamna El-Rufa'i ya yaba wa jami'an sojin da suka gudanar da wannan aiki har aka asamu nasara.
Sannan ya kara jawo hankalinsu a kan su cigaba da rike wannan nasarar da suka samu domin kakkabe dukkan wasu yan bindiga a sansanin su da aka sani.
Wane wurin ne Maikwandaraso?
Maikwandaraso yana kusa da kauyen Karshi kuma ya haɗa iyaka da manyan dazuzzukan Kawara da Malul duk a karamar hukumar Igabi.
Wurin sananne cewa yan bindiga na zama a yankin kasancewar yana kusa da manyan dazuka biyu.
Sojoji sun dakile harin yan bindiga a Zangon Kataf
A wani labarin kuma Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa aƙalla mutum biyar aka kashe a wasu hare-haren da yan bindiga suka kai jihar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa shine ya bayyana haka, ymya kara da cewa dakarun sojoji sun dakile yunkurin kai harin.
Asali: Legit.ng