Abin da Gwamnati za ta yi kafin mika Abba Kyari ga jami'an Amurka – Ministan shari’a, Malami

Abin da Gwamnati za ta yi kafin mika Abba Kyari ga jami'an Amurka – Ministan shari’a, Malami

  • Ministan shari’a, Abubakar Malami ya tabo batun zargin da ke kan Abba Kyari
  • Abubakar Malami ya ce akwai yarjejeniya tsakanin kasar Amurka da Najeriya
  • Minista ya ce Abba Kyari ba zai shiga Amurka ba har sai kotu ta yanke hukunci

Abuja - Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya yi magana game da zargin da ake jifan babban jami’in ‘dan sanda, Abba Kyari da shi.

Dokar kasa za ta yi aiki a kan Abba Kyari

Legit.ng ta samu labari Abubakar Malami ya ce dokar kasa ce za ta yi aiki wajen hukunta Abba Kyari.

Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan rediyon Voice Of America (VOA) a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, 2021.

Akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Amurka?

Abubakar Malami yake cewa duk da akwai yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kasar Amurka, za a bar doka ta yi aiki sarai wajen hukunta Kyari.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

“Eh, akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Amurka a kan taso keyar duk wanda aka samu ya aikta laifi a cikin kasashen; Amrka ko Najeriya.”

Babban lauyan gwamnatin tarayya ya ce hukuncin da kotu ta yanke shi ne zai yi tasiri wajen mika jami’in tsaron ga hukumomin Amurka da ke tuhumarsa.

Abba Kyari da Hushpuppi
DCP Abba Kyari da Hushpuppi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Amma akwai sharuda, sharudan su ne duk lokacin da kasa ta rubuta wa ma’aikatar kasar waje, ma’aikatar za ta aika wa ministan shari’ar shari’a takara domin kotu ta bada dama a dauke wanda ake zargi ya tafi Amurka, domin ya amsa tambayoyi.”
“Ba na cewa za a damka Abba Kyari ga masu neman shi, amma doka za ta yi aiki da kyau kafin a dauki wani mataki.”

Jaridar The Nigerian Lawyer ta rahoto Ministan shari’an ya na cewa sai Alkalai sun bada dama sannan Kyari zai tafi Amurka ya amsa zargin da ke wuyansa.

Da wannan matsaya da Mai girma Ministan ya dauka, ya nuna gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta zabi bangare a shari’ar Ramon Azeez watau Huspuppi ba.

Kara karanta wannan

Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

An dakatar da Kyari daga aiki

A baya an ji labari cewa Hukumar da ke kula da ayyukan 'yan sanda ta kasa, PSC ta dakatar da Abba Kyari kan zarginsa da hannu a badakalar Hushpuppi da FBI.

Dakatarwar DCP Kyari ta fara aiki ne daga ranar Asabar, 31 ga Yuli, 2021, kuma za a ci gaba da sauraron sakamakon binciken da kwamitin da aka nada yake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel