‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mahaifi da tsohuwar Shugaban Majalisa a Zamfara

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Mahaifi da tsohuwar Shugaban Majalisa a Zamfara

  • ‘Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban majalisar dokoki a jihar Zamfara
  • Miyagun sun dauke kishiyar mahaifinsa da wasu ‘yanuwan Nasiru Magarya
  • An dauki tsawon lokaci ana fama da matsalar rashin tsaro a yankin Zamfara

Zamfara - Wasu da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne, sun dauke tsohon da ya haifi shugaban majalisar jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.

'Yan bindiga sun dauke 'yanuwan Rt. Hon. Nasiru Muazu Magarya

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wadannan miyagun mutane, sun kuma yi awon-gaba da wasu ‘yan uwan shugaban majalisar dokokin Zamfara.

Rahoton ya ce daga ciki akwai kishiyar mahaifiyarsa da kawunsa da mutane hudu a sabon harin da aka kai a garin Magarya, a karamar hukumar Zurmi.

Shugaban majalisar dokoki mai ci shi ne yake wakiltar mazabar Zurmi ta gabas a majalisar Zamfara.

Salihu Zurmi mai wakiltar Zurmi ta yamma a majalisar dokoki ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa ‘yan bindiga sun kawo wa Zurmi hari a yammacin Laraba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Honarabul Salihu Zurmi ya ke cewa harin na ranar 4 ga watan Agusta, 2021, shi ne karo na hudu da aka yi ta’adi a kauyukan Zurmi cikin ‘yan kwanakin nan.

‘Yan bindiga
Jami'an tsaron Najeriya Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

“Na farko sun kashe wasu mutane, na biyu sun shiga gidajen mutane, sun dauke masu dabbobi da wasu dabbobin gida.”

Za mu fitar da jawabi - Majalisa, 'Yan sanda

Da aka tuntubi darekta janar na harkokin yada labarai na majalisar dokokin Zamfara, Mustapha Jafaru Kaura, yace za su fitar da sanarwa a game da lamarin.

Alhaji Mustapha Jafaru Kaura ya ce yana tare da mai girma shugaban majalisar jihar Zamfara, ya bukaci a bada lokaci kafin a fitar da jawabi ga manema labarai.

Haka zalika da aka tuntubi rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, kakakin jami’an tsaron, SP Muhammad Shehu ya ce za su fitar da jawabi ba da dade wa ba.

Dazu kun ji cewa ‘Yan Sanda sun koma kotu da Evans, wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane tare da wasu mutane, har da tsofaffin jami'an sojoji biyu.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Cire Kakakin Majalisar Dokoki Daga Wani Mukami

Da aka shiga kotu, Evans ya sanar da Alkali cewa sana’ar saida kayan ado yake yi ba satar mutane ba. Za a cigaba da sauraron wannan shari'a a watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel