Ni ‘dan kasuwa ne, babu abin da ya hada ni da garkuwa da mutane inji Evans a Kotu

Ni ‘dan kasuwa ne, babu abin da ya hada ni da garkuwa da mutane inji Evans a Kotu

  • Jami’an 'yan sanda sun cigaba da shari’a da Chukwudimeme Onwuamadike ‘Evans’
  • Chukwudimeme Onwuamadike ya musanya zargin ya na yin garkuwa da mutane
  • Onwuamadike yace shi ‘dan kasuwa ne a Legas, kuma babu mai kiransa da Evans

Legas - Lauyoyin da suka tsaya wa Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans da sauran mutum biyar da ake kara sun gama kare kansu a kotu.

The Cable ta rahoto yadda shari’ar Chukwudimeme Onwuamadike wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane ta ke tafiya a babban kotu na Ikeja, Legas.

An cigaba da sauraron shari'ar a Legas

Onwuamadike da duk sauran mutanen da ake zargin abokan aikinsa ne, sun musanya zargin da ake yi masu, Evans ya fada wa Alkali cewa shi ‘dan kasuwa ne.

“Ina zama ne a layin Fred Shoboyede, unguwar Magodo Phase II, Legas. Ni ‘dan kasuwa ne, ina harkar kayan ado ne.
“Alkali mai shari’a, ba suna na Evans ba, kuma ba ni da wani lakabi da aka yi mani.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

A zaman shari’ar, wasu tsofaffin sojojin Najeriya, Ifeanyi da Aduba ake zargi da hada-kai da wanda ake tuhuma, sun karyata laifin da ake jifan su da shi.

Chukwudimeme Onwuamadike
Chukwudimeme Onwuamadike (Evans) Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Aduba ya ce wani jami’in ‘dan sanda mai suna Idowu Haruna ya bukaci ya sa hannu a takardar da ke nuna ya aikata laifi, amma sai ya ki yarda da ya yi hakan.

A cewar Aduba, a dalilin taurin kan da ya yi ne Idowu Haruna ya turke shi, ya rika gallaza masa azaba; ya yi masa mugun duka, har ya ji masa rauni da adda.

A karshe Aduba ya amsa laifin cewa yana taimaka wa wajen satar mutane da niyyar a biya kudin fansa ne bayan ya ga jami’an tsaro sun hallaka mutane hudu.

Jaridar ta ce Alkali Hakeem Oshodi ya ba lauyoyin kowane bangare kwana 30 su yi korafi da martani. Za a cigaba da shari’a a ranar 5 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bakare: Abokin tafiyar Buhari ya ba shi shawarar abin yi, ya daina sukar shugabannin baya

Laifin me ake zargin Evans ya aikata?

Ana tuhumar Evans tare da Uche Amadi, Ogechi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi, Okwuchukwu Nwachukwu da Victor Aduba ne da laifin sace Donatus Dunu.

Lauyoyin da suka shigar da kara a kotu sun ce wadannan mutane sun karbi £223,000 (Naira miliyan 100) kafin su saki Donatus Dunu, an yi haka ne a 2017.

Tun a watan Yunin 2017 ne Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani jami’in soja da yake taimaka wa Evans wajen satar mutane, ana karbar fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel