Gwamnatin Buhari ta yafewa MTN haraji, kamfanin zai gyara titin da ya yi raga-raga a Najeriya

Gwamnatin Buhari ta yafewa MTN haraji, kamfanin zai gyara titin da ya yi raga-raga a Najeriya

  • Kamfanin MTN ne zai dauki nauyin gyaran hanyar Onitsha zuwa Enugu
  • Gwamnatin Tarayya ta yafe wa MTN bangare a cikin harajin da ke kansa
  • MTN Nigeria ya amince ya shiga tsarin RITC da gwamnati ta shigo da shi

Najeriya - Babban kamfanin sadarwar kasar nan, MTN Nigeria ya bada sanarwar gyara babban titin Enugu zuwa garin Onitsha da zai ratsa Enugu da Anambra.

The Cable ta ce kamfanin zai yi wannan ne a karkashin tsarin RITC da aka shigo da shi na gina tituna da kudin harajin da ya kamata hukumar FIRS ta karba.

Shugaban MTN Nigeria, Karl Toriola, ya bayyana wannan a rahoton da ya fitar na sakamakon kasuwancin da kamfanin ya yi daga farkon shekara zuwa yau.

Rahoton ya bayyana cewa kamfanin MTN Nigeria ya fitar da ribar da ya samu a shafin hada-hada da zuba hannun jarin Najeriya a ranar 30 ga watan Yuni, 2021.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

MTN Nigeria za su gyara babban titin Onitsha - Enugu

“A 2021 ne kamfanin MTN yake cika shekara 20 a Najeriya. Yayin da mu ke bikin wannan dade wa, mu na farin cikin bada sanarwar cewa darektocinmu sun amince mu shiga tsarin RITC."

Titin Onitsha zuwa Enugu
Titin Onitsha zuwa Enugu Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

“Hakan na zuwa ne a dalilin yunkurin gwamnati na yin amfani da tsarin PPP wajen gyara hanyoyi masu muhimmanci a Najeriya. Mu na shirin mu yi aikin gyaran titin Enugu zuwa Onitsha.”
“An fara wannan tattauna wa yanzu haka, kuma za a ji sanarwar yadda ta kasance nan gaba.”

Karl Toriola ya ce MTN Nigeria zai kashe Naira biliyan 640 nan da shekaru uku domin a inganta fasahar sadarwa kamar yadda gwamnati ta ci buri nan da 2025.

Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin RITC ne da nufin kamfanoni da ‘yan kasuwa su rika gyara hanyoyin kasar nan a madadin hukuma takarbi haraji a hannunsu.

Kara karanta wannan

Ana neman mafita, Jigon APC ya dumfari kotu, ya na so a tsige Buni, duk shugabannin Jam’iyya

Wannan shiri na PPP da gwamnati za ta hada-kai da kamfanoni zai taimaka wajen gyara da gina tituna domin ayi maganin karancin hanyoyin da ake da su a Najeriya.

A irin wannan tsari ne kwanakin baya gwamnatin tarayya ta ba Dangote kwangilar yin wasu hanyoyi biyar da za su ci Naira biliyan 300 a maimakon ya biya haraji.

Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Fashola ya ce Dangote zai gina tituna a Kaduna, Borno, da Legas a maimakon ya gwamnati ta karbi haraji a hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel