Ana neman mafita, Jigon APC ya dumfari kotu, ya na so a tsige Buni, duk shugabannin Jam’iyya

Ana neman mafita, Jigon APC ya dumfari kotu, ya na so a tsige Buni, duk shugabannin Jam’iyya

  • Okosisi Emeka Ngwu ya kai karar jam’iyyar APC a babban kotun tarayya
  • ‘Dan Jam’iyyar ya na so Alkali su ruguza kwamitin riko na Mai Mala Buni
  • Lauyan Okosisi Emeka Ngwu ya ce doka ba ta san da zaman kwamitin ba

Abuja - Wani fusataccen ‘dan jam’iyyar APC mai mulki, ya bukaci kotun tarayya da ke zama a Abuja ta tsige shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar.

Okosisi Emeka Ngwu ya nemi kotu ta yi watsi da duk wasu matakan da APC tun daga lokacin da gwamna Mai Mala Buni ya zama shugaban rikon kwarya.

Daily Trust ta ce Okosisi Emeka Ngwu ya shigar da kara mai lamba FCT/HC/CV/1824/2021 a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021, a gaban babban kotun.

Akwai kwamitin rikon kwarya a tsarin mulkin APC?

Lauyan da ya shigar da wannan kara, Oba Maduabuchi (SAN), ya fada wa kotu cewa kwamitin rikon kwarya da gudanar da zabe bai da gindin-zama a APC.

Kara karanta wannan

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

Oba Maduabuchi SAN ya ce doka da tsarin mulkin APC bai san da zaman wannan kwamitin ba.

Lauyan ya ce a dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima, majalisar koli ta NEC ce kurum za ta iya tsara lokacin da za ayi zaben shugabanni da ‘yan takara.

Taron APC
Shugabannin APC a taron NEC Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Rahoton ya ce babban lauyan ya dogara ne da sashe na 87(4)(b)(1) na dokar zabe. Har yanzu kotu ba ta sa ranar da za a fara sauraron wannan shari’ar ba.

Okosisi Emeka Ngwu ya na karar kwamitin Buni

Jaridar The Naton ta ce wadanda lauyoyin Okosisi Emeka Ngwu suke kara a kotun sun hada da jam’iyyar APC da duka ‘yan kwamitin na rikon kwarya.

‘Yan kwamitin su ne: Gwamna Mai Mala Buni, Adegboyega Oyetola, Gwamna Abubakar Sani-Bello, Ken Nnamani, Stella Okorete da Dr. James Lalu.

Ragowar sun hada da: Sanata Abubakar Yusuf; Akinyemi Olaide; David Leon; Abba Ali; Farfesa Tahir Mamman; Ismail Ahmed da John Akpanudoedehe.

Kara karanta wannan

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

A makon nan kun ji labari cewa shari’ar da ake yi a kotu sun hana jam’iyyar APC iya gudanar da zaben shugabanni na mazabu a jihohin Bayelsa da Imo.

Haka zalika zaben kanshiloli da shugabannin kananan hukumomi sun sa an daga zabukan APC a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng