Kungiyar Ibo ta ce Bayarabe bai isa ya nemi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ba

Kungiyar Ibo ta ce Bayarabe bai isa ya nemi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ba

  • Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta na goyon bayan Ibo su karbi mulki a 2023
  • Kungiyar ta ce ba Bayarabe ne ya kamata ya canji Muhammadu Buhari ba
  • Kakakin Ohanaeze Ndigbo yace Yarbawa sun dana shugabancin Najeriya

Kungiyar nan ta Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta ce ‘yan kudu maso yamma ba su da damar da za su nemi shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta na kafa hujja da cewa Yarbawa sun rike mulki na shekaru takwas a lokacin Olusegun Obasanjo.

Baya ga haka, yankin na kudu maso yamma za su samu damar shekara takwas tsakanin 2015 da 2023 ta hannun mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta ce ‘yan siyasar Ibo ne suka fi dace wa su dare kujerar shugaban kasa a 2023, ta nemi al’umma su mara masu baya.

Jawabin da kungiyar ya fito ta bakin sakatarenta, Okechukwu Isiguzoro, wanda ya yi tir da masu neman jawo wa Ibo cikas saboda wasu na fafutukar Biyafara.

Kara karanta wannan

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

Gangamin APC
Gangamin APC a Legas Hoto: businesspost.ng
Asali: UGC

Jawabin da Okechukwu Isiguzoro ta fitar

“Kudu maso yamma ba su da hakki ga kujerar shugaban kasa a 2023. Cif Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007.”
“Farfesa Yemi Osibanjo zai shafe shekaru takwas a kujerar mataimakin shugaban kasa tsakanin 2015 da 2023.”
“Saboda haka 2023, lokaci ne da mutanen Ibo za su hau kan kujerar shugaban kasar Najeriya.”

Danyen aikin IPOB zai kawo wa Ibo cikas?

“Shin ta’adin OPC ya hana Olusegun Obasanjo samun mulki a 1999. Danyen aikin tsagerun Neja-Delta ya hana Goodluck Jonathan zama shugaban kasa a 2011? ‘Yan ta’addan Boko Haram sun hana Buhari mulki a 2015?”

Okechukwu Isiguzoro ya ce tun da wadannan kungiyoyi ba su hana ‘yan yankin yin mulki ba, bai dace a kafa hujja da wannan, a hana su kujerar shugaban kasa ba.

Ku na da masaniya cewa ana fama da rikicin cikin-gida a jam'iyyar APC. Har ta kai an bar Farfesa Yemi Osinbajo da neman hanyar da za a dinke barakar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

Jam’iyyar APC ta na tsoron hukuncin kotun koli ta ci ta, mataimakin shugaban kasar da wasu shugabanninta su na neman mafita domin gudun a samu matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel