Saura kiris ‘Yan bindiga su hallaka Basarake a kan hanyar dawowa daga taron sulhu
- ‘Yan bindiga sun tare motar Hakimin Bassa, Daniel Chega a jihar Filato
- An taki sa’a ba a rasa rai a wannan hari da aka kai wa Mai martaban ba
- Miyagun sun yi wa motar Mai martaba Chega kaca-kaca da bindigogi
Wani mai rike da sarautar gargajiya a karamar hukumar Bassa, jihar Filato, Daniel Chega, ya taki sa’a yayin da ‘yan bindiga su ka kai wa motarsa hari.
The Nation ta rahoto cewa basarake ya sha da kyar a harin da aka kai masa yayin da yake hanyar gida bayan halartar wani taro a kan batun rashin tsaro.
Daniel Chega ya gamu da wannan jarrabawa ne bayan ya tashi daga wani zama da aka kira da ‘yan bindiga da mutanen gari domin samun zaman lafiya.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe 'Dan Sarkin Kontagora a Neja
Yadda abin ya auku - Shugaban matasa
Wannan lamari ya auku ne da kimanin karfe 4:30 na yamma a ranar Litinn, 5 ga watan Yuli, 2021. Amma an yi dace babu wanda ya rasa ransa a wannan harin.
Jaridar The Eagle ta ce Daniel Chega shi ne hakimin Miango da ke karkashin karamar Bassa, kuma ya na kokarin kawo karshen ta’adin da ake yi a kasarsa.
Shugaban kungiyar matasa da cigaban garin Miango, Ezekiel Bini, ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa an kai wa hakimin na kasar Miango hari ido na ganin ido.
Mista Ezekiel Bini ya halarci wannan zama da aka yi a babban birnin Filato, Jos, inda ya ce Ubangiji ne kawai ya yi cewa mai martaban zai tsira da ransa.
“Ikon Allah ne kurum da hakimin ya tsira. Mu na tare da shi wajen taron tsaro da sulhu. Kun san cewa an rasa mutane da dukiyoyin miliyoyi a garin Miango.”
Ezekiel Bini ya ce an yi wannan asara ne a sanadiyyar barnar da miyagun ‘yan bindiga su ke yi.
KU KARANTA: Jami’ar Legas ta yaye ‘Yar shekara 71 da ta kammala Digirin PhD
“Saboda haka, da nufin a samu wanzajjen zaman lafiya ne hukumar jiha ta shirya wani taro a kan harkar tsaro da Fulani da sauran mutanen gari a ranar Litinin.”
Yayin da motarsa ta doshi wani barikin sojoji a hanya, sai ‘yan bindiga su ka yi masa kwanton-bauna, su ka yi wa motarsa kirar peugeot 406 rugu-rugu da harsashi.
Ku na da labari cewa Jihohin Katsina da Zamfara a yankin Arewa suna fuskantar barazanar kashe-kashe da masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga su ke ta yi.
A dalilin haka Sarakuna da masu rike sarautar gargajiya akalla bakwai su ka rasa rawani. Daga ciki har da Sarakunan Zurmi, Maru da Dansadau da hakimi a Katsina.
Asali: Legit.ng