Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci

Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci

  • Yau Kwana na biyu da Likitoci a Najeriya suka sake shiga yajin aiki
  • Likitocin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawuranta
  • Gwamnatin tarayya na kira da Likitocin suyi hakuri su koma teburin sulhu

Abuja - Karamin Ministan Lafiya, Dr. Olorunimbe Mamora, a ranar Talata, ya yi kira ga shugabannin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD su koma teburin sulhu.

Gwamnati tace tana iyakan kokarinta wajen canza tunanin da ake mata a bangaren lafiya.

Mamora ya bayyana hakan ne a taron kungiyar likitoci NMA, shiryar birnin tarayya, rahoton Punch.

Tace:

"Gwamnati na kokarin kawo gyara. Ba zai yiwu muyi kasa a gwiwa ba. Ina amfani da wannan dama in yi kira ga Likitocin dake yajin aiki yanzu su dawo teburin sulhu saboda a tattauna dukkan matsalolin."
"Wannan shine roko na. Ko a faggen yaki, abokan adawa a karshe na komawa teburin sulhu domin tattauna matsaloli."

Kara karanta wannan

Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce

Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci
Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci

Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti

Yan uwa na kwashe marasa lafiyansu daga asibitocin gwamnati yayinda yajin aikin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) ya shiga kwana ta biyu.

Jaridar Sun ta bayyana cewa a asibitocin da ta ziyarta, Likitoci sun dauke kafa gaba daya kuma an bar marasa lafiya babu mai duba su.

Hakazalika an fadawa wadanda suka kawo sabbin marasa lafiyansu su tafi asibitoci masu zaman kansu.

Likitoci a Najeriya sun tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Kungiyar likitoci a kasar nan (NARD) ta umurci mambobinta dasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin, 2 ga watan Agusta.

Da yake yiwa yan jarida bayani a karshen taron, Shugaban kungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng