Ni na yi magana da Malam Jafar karshe kafin a kashe shi - Salim Jafar Adam ya tuna 2007

Ni na yi magana da Malam Jafar karshe kafin a kashe shi - Salim Jafar Adam ya tuna 2007

- A shekarar 2007 wasu ‘Yan bindiga su ka harbe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

- Babban ‘Dan da ya bari a Duniya ya bayyana yadda yake kewar Mahaifin na su

- Saleem Ja'afar Adam ya ce da shi Malam ya yi magana a karshe kafin ya mutu

Babban ‘dan Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, Saleem Ja'afar Mahmud Adam ya yi hira da BBC Hausa, inda ya yi magana a kan mahaifinsa da aka kashe.

Saleem Ja'afar Mahmud Adam ya bayyana wa ‘yan jarida cewa shi ne wanda ya yi magana da Malam a cikin iyalinsa a asubar da aka kashe shi a masallaci.

BBC ta yi hira da Saleem Ja'afar Mahmud Adam ne a ranar 14 ga watan Afrilu, 2021. A wannan rana aka cika shekara 14 da kashe babban malamin musuluncin.

KU KARANTA: Cikakken tarihin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

“Ni ne kusan wanda ya yi magana da shi karshe a cikin ‘ya ‘yansa, ya tada ni in tafi masallaci, kafin na kai ga zuwa masallaci, abin da ya faru, ya faru.” Inji Saleem.

“Ban kai shekaru na mallakar hankali na ba, amma zan iya tuna wa cewa wannan ranar ba karamin tashin hankali aka shiga ba.” Saleem ya ce abin ya zo kwatsam.

Wannan matashi ya ce Mahaifinsu bai samun isasshen lokaci da yake raye, amma ya maida hankali sosai wajen ganin sun samu ilmin musulunci da na rayuwa.

Saleem ya ce sun samu taimakon na-kusa da mahaifinsu: “Malam ya kasance ya na da aminai da ‘yanuwa na gari, sun yi kokari tsayin-daka na ganin mun samu ilmi.”

KU KARANTA: Ana tunawa da Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Ni na yi magana da Malam Jafar karshe kafin a kashe shi - Salim Jafar Adam ya tuna 2007
Marigayi Jafar Mahmud Adam da Salim Jafar Adam
Asali: UGC

“Babu abin da za mu ce sai da mu gode masu, mu saka masu, Allah ya sa a cikin mizaninsu.” Saleem ya ce har gobe ya na amfana da karatun da tsohonsu ya yi.

“Duk lokacin da na tuna da shi, na kan ji kewan rashinsa a matsayinsa na uba, musamman a lokacin da mutum yake neman shawarar mahaifi kan gogayyar rayuwa."

A cewar Saleem Ja'afar Mahmud Adam, babu abin da ya ke burge shi kamar ya ji ana sauraron karatun mahaifinsu, ya ce hakan ya na nufin Shehin ya shuka abin alheri.

A shekarar da ta gabata ne ku ka ji cewa Allah ya yiwa AbdulMalik Jafar Adam, 'dan babban malamin nan da aka yi, Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam, rasuwa.

Manyan malamai irinsu Dr Isa Ibrahim ali Pantami, wanda yanzu haka shi ne ministan sadarwa, Sheikh Abdullah Gadon Kaya da Dr. Mansur Sokoto su ka sanar da rasuwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel