Babban Limamin Najeriya, Maqary ya yi barazanar kai Shehin da yi masa 'kazafi' gaban Alkali
- Farfesa Ahmad Maqary ya yi wa Abdallah Gadon Kaya raddi a kan wasu kalamansa
- Babban Limamin ya bukaci Abdallah Gadon Kaya ya fito da wata waya da yace ya yi
- Ahmad Maqary yace zai tafi kotu, sannan ya nemi a fito da kalaman da ya yi a salula
Abuja- Limamin babban masallacin Najeriya da ke birnin tarayya Abuja, Ahmad Ibrahim Maqary ya maida martani a kan wani zargi da aka jefe sa da shi.
A jawabin da Farfesa Ahmad Ibrahim Maqary ya yi, wanda aka wallafa a shafin Al Minhaj a Facebook, shehin ya tabo batun zargin da wani ya yi masa.
Ahmad Maqary bai ambaci sunan malamin da yake zargi da yi masa kazafi ba, amma alamu sun nuna ya na martani ne ga Abdallah Umar Gadon-Kaya.
Farfesa Maqary yake cewa bai so ya kai kara ba, zai fi so a ce Ubangiji ne ya yi shari’a, amma hakan ya zama dole saboda kubutar da addinin musulunci.
Malamin ya ce cikin biyu ya zama dole ayi daya, ko wanda ya yi wannan magana ya gabatar da uzuri, ya bada hakuri, ko ya kawo hujjojinsa a dakin shari’a.
“Ba babin kare kai ba ne wannan, saboda al’umma ta san wurin wa za ta dauki addininta.”
Maqary yace sabaninsa da wannan malami bai da alaka da bambancin fahimta kamar yadda aka ga al’umma sun hadu wajen yi wa Abduljabar Kabara raddi.
Menene abin da Dr. Abdallah Umar Gadon-Kaya ya fada?
A wata hudubar Juma’a da ya yi a Kano, Dr. Abdallah Umar Gadon-Kaya ya yi ikirarin limamin ya yi wasu maganganu a lokacin da aka yanke wa wanda ya yi wa addini batanci hukunci a kotu.
Abdallah Gadon-Kaya ya na zargin limamin babban masallacin na Abuja da saba wa sauran malaman musulunci, bayan tsokacin da ya yi a kan mukabalar da aka yi da Abduljabbar Kabara.
Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’
Wani raddin Farfesa Ahmad Ibrahim Maqary ya yi masa?
“Za a fito da wayar da na yi domin a yada wa Duniya, daya daga ciki har na nemi izininsa, ni da mutum biyu kadai na yi waya; daya jagoran addini ne, daya ‘dan kasuwa ne.”
“An fara aikin fito da maganar da mu ka yi daga kafar sadarwa, za a saki ga Duniya.”
“Ina tunanin wanda zai yi wannan abin (da ake zargi), bai cancanta da wannan kujera ba.”
Abdallah Umar Gadon-Kaya ya ki cewa uffan
Legit.ng Hausa ta nemi jin ta bakin shehin malami, Dr. Abdallah Umar Gadon-Kaya a ranar Laraba, a kan wannan lamarin, amma bai iya cewa komai ba.
Da muka kira Abdallah Umar Gadon-Kaya a wayar salula, ya ce ba zai yi magana a kan batun ba.
Asali: Legit.ng