Dattijon Arewa ya fadi ainihin dalilin da ya sa EFCC ta sake biyo wa ta kan Bukola Saraki

Dattijon Arewa ya fadi ainihin dalilin da ya sa EFCC ta sake biyo wa ta kan Bukola Saraki

  • Tanko Yakasai ya yi tsokaci game da tsare Bukola Saraki da Jami’an EFCC suka yi
  • Yakasai wanda ya na cikin dattawan kasar nan yana ganin akwai siyasa a lamarin
  • Dattijon ba zai so wani abin ya taba ‘'dansa' kuma ‘dan abokin tafiyarsu a siyasa ba

Kano - Fitaccen dattijon nan, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi magana game da gayyatar da hukumar EFCC ta yi wa tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki.

Jaridar Punch ta rahoto Tanko Yakasai ya na cewa siyasa ce ta sa jami’an EFCC ta ke bibiyar tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.

Da yake magana da ‘yan jarida a garin Kano a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021, Tanko Yakasai yace ana neman hana Saraki yin takara ne a 2023.

Anya babu siyasa a lamarin nan?

“Na karanta labari a kafar sadarwa na zamani cewa EFCC ta gayyaci yarona, kuma ‘dan abokina, marigayi Dr. Olusola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki a ranar Asabar da ta wuce.”

Kara karanta wannan

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

“Ba zan sa kai na a kan duk wani abu da zai taba binciken ko hana doka ta yi aiki ba. Amma ina fatan cewa wannan yunkuri da EFCC ta ke yi ba na siyasa ba ne.”
“Ina fatan bai da alaka da zabe mai zuwa da za ayi a kasar nan.”

Buhari da Bukola Saraki
Bukola Saraki tare da Shugaban kasa Hoto: insidebusiness.ng
Asali: UGC

Bukola Saraki kamar ‘da yake a wurin Tanko Yakasai

“Bukola ‘da na ne ta wurare dabam-dabam, ‘dan abokina ne a siyasa, shugaban masu rinjaye a majalisa a jamhuriyya ta biyu, Dr. Olusola Saraki.”
“Bayan haka Bukola abokin babban ‘dan ciki na ne.”

A dalilin wadannan alaka da kare hakkin jama’a, dattijon mai shekara 94 yake cewa ya damu da halin da ‘dan siyasar yake ciki, bai goyon bayan a ci masa zarafi.

This Day ta rahoto Yakasai yana cewa ya na fatan abin da aka fara ba zai sa a soma yi wa ‘yan adawa barazana ba, ya ce shi ba ya goyon bayan wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

Saraki ya fada hannun EFCC

A makon da ya wuce ne Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arziki zagon kasa watau EFCC ta tabbatar cewa ta tsare tsohon gwamna Bukola Saraki.

Dr. Bukola Saraki ya yi karin-haske daga baya, ya ce ba kama shi aka yi ba, sai dai kawai ya kai kansa gaban jami'an EFCC ne domin ya yi masu wasu bayani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng