Saraki na hannunmu, Hukumar EFCC ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa

Saraki na hannunmu, Hukumar EFCC ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa

  • Hukumar EFCC ta ce Bukola Saraki na hannunta
  • Wannan ya biyo bayan damke Sanata Tanko AlMakura na Nasarawa
  • EFCC tace yanzu haka yana hannunta kuma tana masa tambayoyi

Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a ranar Asabar a Abuja ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa an gayyaci Saraki ne domin yi masa tambayoyi kan zargin almundahana da babakeren wasu kudade.

Ya ce Saraki yanzu haka na hannunsu kuma suna yi masa tambayoyi.

Mun kawo muku cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tsare tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, bisa zargin sata da handame kudade.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tsare Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara a ranar Asabar, majiyoyin da suka shaida hakan sun ce, lamarin ka iya haifar da wani tashin hankali ga dan siyasar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa

Saraki na hannunmu, Hukumar EFCC ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa
Saraki na hannunmu, Hukumar EFCC ta tabbatar da damke tsohon shugaban majalisar dattawa
Asali: Original

An damke Tanko Al-Makura

Labarin damke Saraki ya biyo bayan damke tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, da uwargidarsa Mairo.

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaida cewa jami'an EFCC sun yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja kan zargin rashawa.

Amma Tanko Al-Makura ya karyata jita-jitan dake yawo inda yace hukumar ta gayyace shi ne kan wasu korafe-korafe da ake akansa, inda ya yi tattaki yaje ofishin hukumar ya gana da shugabanta da wasu jami'anta cikin kankanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel