Yan Najeriya su shiryawa mumunan ambaliyar ruwan sama tsakanin Agusta da Oktoba, Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin tarayya ta yi kira ga yan Najeriya su shiryawa mumunan ambaliya
- An ambaci jerin jihohin da ka iya fuskantar wannan ambaliya
- Ministan ruwa da shugaban hukumar NIHSA sunce gwamnatocin jiha su gyara magudanun ruwa
Yan Najeriya su shiryawa mumunan ambaliyar ruwan sama
Hukumar ayyukan ruwan Najeriya (NIHSA) ta yi hasashen cewa tsakanin watan Agusta da farkon Oktoba, za'ayi mumunan ambaliyan ruwan sama a Najeriya.
NIHSA tace ambaliyar zata munana a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, rahoton DT.
Dirakta Janar na hukumar, Injiniya Nze Clement Onyeaso, a hirar da yayi da manema labarai a Abuja, ya ce dukkan jihohin da aka ambata a farkon shekara zasu fuskanci ambaliya su shirya.
Ya yi kira ga yan Najeriya su shiryawa wannan ambaliya ta hanyar gyara magudanun ruwa tare da cire bola, ciyayi, gansakuka dss.
Muna hasashen za'ayi ambaliya a jihohi 28 bana, Gwamnatin tarayya ta lissafo su
A watan Mayu, anyi hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28 a bana, sabon rahoton hasashen ambaliya AFO ya nuna.
Ana fitar da wannan rahoto ne a kowani shekara.
Jihohin da aka lissafo sune,Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.
Ministan arzikin ruwa, Suleiman Adamu, ya lissafa wadannan jihohi ne ranar Alhamis a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA).
Asali: Legit.ng