Gwamnati ta na so a rage farashin ‘Data’ da 60% nan da shekaru 3 zuwa 5

Gwamnati ta na so a rage farashin ‘Data’ da 60% nan da shekaru 3 zuwa 5

- Shugaban hukumar NCC ya ce su na shirin sake rage farashin ‘Data’

- Ma’aikatar sadarwa ta ci burin yin wannan aiki nan da shekarar 2025

- Duk da haka Najeriya ta na cikin kasashe masu arahar ‘Data’ a Afrika

Shugaban hukumar NCC mai kula da sadarwa, Umar Danbatta, ya ce ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta na shirin rage farashin ‘data’.

Data shi ne abin da ake saida wa masu hawa shafukan yanar gizo da manhajojin sada zumunta.

Hukumar NCC ta bayyana haka ne a lokacin da shugabanta ya yi magana da ‘yan jarida a Kano. NCC ta ce su na kokarin rage kusan 60% na kudin ‘data’.

KU KARANTA: Tsageru sun yi awon gaba da kaya masu guba a Kaduna

Farfesa Umar Danbatta ya ce za a koma saida kowane 1GB a kan N390, a maimakon N1, 000. Farfesan ya ce wannan ya na cikin dogon burin NCC.

A wannan shiri da NCC ta ke yi na 2020 – 2025, na’urorin 4G za su karade Najeriya, sannan za ayi kokarin ganin karfin hawa yanar gizo ya shiga ko ina.

Farfesan ya na mai cewa, an ba ma’aikatar sadarwa nauyin ganin an bullo da dabaru ta yadda kamfanonin MNO za su rage kudin da su ke saida ‘data’.

Danbatta ya ce ana so a rage tsadan ‘data’ daga N1, 000 da aka saba saye zuwa N390. Wannan duk da kokarin da aka yi na rage farashin a kwanakin baya.

KU KARANTA: Zanga-zanga: Na kira Buhari sau biyu ban same shi ba - Sanwo Olu

Gwamnati ta na so a rage farashin ‘Data’ da 60% nan da shekaru 3 zuwa 5
Umar Garba Danbatta Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Hakika farashi ya ragu zuwa kowane 1GB a kan N1, 000, amma gwamnati ta ce mu yi harin N390 nan da shekaru uku zuwa shekaru biyar.” Inji Danbatta.

Kafin a iya samun wannan rangwame, sai gwamnati ta gina abubuwan da ake bukata. A halin yanzu kasashen Afrika kadan su ka fi Najeriya arahar ‘data’.

Kwanakin baya Ministan sadarwa ta tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami ya bada labarin yadda ake tara masa takardun neman aiki a duk jihar da ya je.

Dr. Isa Pantami ya ce daga ya kai ziyara jihohi sai a rika mika masu takardun masu neman aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel