DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Shahrarren madamfari Huspuppi

DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Shahrarren madamfari Huspuppi

  • Abba Kyari na cikin mutane shida da Hushpuppi ya ambata a kotu
  • Hushpuppi ya yi bayanin yadda Abba Kyari ya taimaka masa wajen kama abokin hamayya
  • Dukkan wannan na kunshe cikin jawabin da gwamnatin Amurka ta saki

Shahrarren mai damfarar yanar gizo, Abbas Ramoni, wanda akafi sani da Huspuppi, ya bayyana cewa hazikin dan sanda, DCP Abba Kyari, na cikin wadanda ya baiwa kudin cin hanci.

Hakan na kunshe cikin wasu takardun kotun gwamnatin Amurka.

Bayan shekara da shekaru yana damfarar jama'a, an damke Hushpuppi a Dubai kuma aka garzaya dashi Amurka.

Jami'an kotu a Amurka sun ce yayin gudanar da bincike, Hushpuppi ya bayyana cewa ya baiwa Abba Kyari kudin cin hanci domin ya tayashi kulle wani dan adawarsa dake Najeriya kan harkallar damfarar wasu yan kasar Qatar $1.1 million.

A cewar jawabin da ma'aikatar Shari'ar Amurka ta saki, Huspuppi ya bukaci Abba Kayri ya kulle masa Kelly Chibuzor.

Kara karanta wannan

Shahararren ‘Dan 419 a Duniya, Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari

A binciken da akayi, an gano Vincent ya tuntubi wanda ake shirin damfara a Qatar cewa damfararsa Hushpuppi zai yi.

Kawai sai Hushpuppi ya fusata ya tuntubi Kyari da ya daure masa Vincent, cewar binciken.

An nakalto Hushpuppi da cewa bayan damke masa Vincent da akayi, Abba Kyari ya turo hotunan yadda suka daureshi tare da lambar asusun bankinsa domin a tura masa kudin aikin.

DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Huspuppi
DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Shahrarren madamfari Huspuppi
Asali: UGC

Takardun kotun suka ce:

"Takardun kotu sun yi bayanin wani rashin jituwa tsakanin masu damfara, inda ake tunanin Vincent ya tuntubi wanda ake kokarin damfara cewa Abbas da Juma na kokarin damfararsa ne."
"Bayan haka Abbas ya shirya yadda Abba Kyari, 46, ya daure Vicent. A cewar takardar rantsuwar (da Abbas yayi), Kyari babban mataimakin kwamishinan yan sandan Najeriya ne wanda akayi zargin shi ya daure Vincent a bisa bukatar Abbas."
"Kuma ya turawa Abbas hotunan kama Vincent. Hakazalika Kyari ya tura akawunt lambarsa ga Abbas domin a tura masa kudin daure Vincent."

Kara karanta wannan

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari

Ramon Abbas, ya amsa laifuffukansa ya yarda bai da gaskiya, a shari’ar da ake yi da shi a Kalifoniya, Amurka.

Punch ta ce Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya amince ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su nan satar kudi, damfara da dai sauransu.

Kamar yadda takardun kotu suka nuna, Ramon Abbas ya tabbatar wa kotu cewa lallai bai da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel