Hushpuppi: Ya kamata Abba Kyari ya je Amurka, ya wanke kan shi kafin a damke shi inji HURIWA
- Human Rights Writers Association of Nigeria ta ba DCP Abba Kyari shawara
- FBI ta na zargin babban ‘Dan sandan da karbar kudi daga hannun Hushpuppi
- Kungiyar HURIWA ta bukaci Kyari ya je har Amurka, ya wanke kanshi a kotu
Amurka - The Nation ta ce kungiyar Human Rights Writers Association of Nigeria wanda aka fi sani HURIWA ta yi magana game da zargin Abba Kyari.
Kungiyar HURIWA ta ba shahararren ‘dan sanda, Abba Kyari shawarar ya tafi kasar Amurka ya wanke kan shi a gaban kotu daga zargin da ake yi masa.
Jaridar The Nation ta rahoto HURIWA ta na wannan jawabi a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, 2021.
Jawabin kungiyar HURIWA
“Amurka kasa ce da ta ke da damukaradiyya mai tsari, inda doka ta ke aiki. Saboda haka idan ana zargin ka da laifi, babu bukatar a wanke ka a gidan jaridu.”
“Abin da ya fi dace wa shi ne, kafin FBI ta yi amfani da jami’an Interpol su yi ram da kai, a matsayinka na mai cewa ka na da gaskiya, sai ka nemi jirgin da zai je Washington ko New York, ka tafi kotu, ka nemi lauyoyi su kare ka a gaban Alkali.”
Wannan kungiya ta masu rubutu domin kare hakkin Bil Adama ta ba DCP Abba Kyari shawarar ya gabatar da takarda, ya karyata zargin da ake yi masa.
HURIWA ta na so jami’in ‘dan sandan ya tashi takanas zuwa Amurka domin ya tabbatar da gaskiyarsa, a madadin ya yi kokarin kare kan shi a jarida.
“Wannan zargi me nauyi ne, kuma an kai maganar zuwa kotu, ba mutane ne za su yi shari’a ba.”
“Mu na ganin a matsayinka na mai ikirarin ba ka da laifi, abin da ya kamata shi ne ka yi maza, ka tashi da kanka, ka tafi kotun Amurka, sai ka wanke kanka.”
Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, babu labarin cewa Abba Kyari ya yi yunkurin zuwa kasar ta Amurka domin ya kare kan shi daga zargin.
Zargin da ke wuyan Abba Kyari
A baya kun ji cewa hukumomin Amurka na zargin 'dan sandan ya amfana da dukiyar Ramon Azeez, wani shahararren 'dan damfara da ake kira Hushpuppi.
Asali: Legit.ng