An Rasa Rayuka Shida Sakamakon Hatsarin Mota Da Ya Ritsa Da Mutum 18 a Bauchi

An Rasa Rayuka Shida Sakamakon Hatsarin Mota Da Ya Ritsa Da Mutum 18 a Bauchi

  • Mummunan hatsarin mota ya faru a hanyar Darazo zuwa Dukku a jihar Bauchi
  • Mutane shida sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu fasinjoji takwas suka jikkata
  • Hukumar FRSC na jihar Bauchi ta tabbatar da afkuwar hatsarin ta kuma ce gudu ne ya janyo hatsarin

Mutane shida ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya faru a ranar Alhamis misalin karfe 11.33 na safe a kan hanyar Darazo zuwa Dukku a jihar Bauchi, Daily Trust ta ruwaito.

Babban kwamandan FRSC na reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatarwa The Punch afkuwar hatsarin.

Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin mota Volkswagen mai lamba KTG-950ZZ da wani Ahmad Umar ke tukawa da wata mota Peugeot Saloon mai lamba AKK-53CB amma ba a san sunan direbanta ba.

An Rasa Rayyuka Shida Sakamakon Hatsarin Mota da Ya Ritsa Da Mutum 18 a Bauchi
Motar bada daukan wadanda suka yi hatsari na hukumar FRSC. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Abin da ya janyo hatsarin?

Abdullahi ya ce tsulla gudu fiye da ka'ida ne ya janyo hatsarin.

Kara karanta wannan

Wasu Matasa 5 Da Ke Shirin Fara Yi Wa Ƙasa Hidima Sun Mutu a Hatsarin Mota a Abuja

Ya ce:

"Hatsarin ya ritsa da mutum 18; 12 manyan maza ne, hudu manyan mata sai kananan yara mata biyu. Mun garzaya wurin da abin ya faru nan take bayan an kira mu domin aikin ceton rai.
"Fasinjoji takwas daga cikinsu; biyar manya maza da uku mata sun samu raunuka. An kuma sanar da yan sandan yankin Darazo."

Ya kuma kara da cewa sauran fasinjojin hudu babu abin da ya same su.

Har wa yau, ya ce an kawar da motocin daga hanya domin sauran motocci su samu saukin wucewa sannan an gano wayoyin salula tara da N20,500 a wurin hadarin.

Shugaban FRSC na Bauchi ya yi wa direbobi gargadi

Shugaban na FRSC ya yi kira ga direbobi su rika tuki cikin natsuwa kuma su dena wuce ka'idar gudun da doka ta tanada musamman a yanzu lokacin damina domin kiyayye rayyuka da dukiyoyin mutane.

Ya ce:

"Na yi mamakin afkuwar hatsari a wannan hanyar domin mikaken hanya ne. Ina kira ga direbobi su kara kiyayewa. Su rika bin dokokin tuki don kiyayye rasa rayyuka da dukiyoyin mutane."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel