Tun bayan daina sayarwa yan canji Dala: Farashin Naira ya fadi karo na biyu
- Farashin Naira na cigaba da fadi a kasuwar bayan fagge
- Bankin CBN ta umurci bankuna ta bude ofishin saye da sayar da Dalar Amurka ga mutane
- Masana sun jinjinawa wannan mataki da gwamnati ta dauka
Lagos - Farashin Naira ya sake sauka 523/$ a kasuwar bayan fagge ranar Laraba, karo na biyu bayan bankin CBN ta sanar da daina baiwa yan kasuwar canji Dalar Amurka.
A rahoton da aka gani a shafin naijabdcs.com, shafin yan kasuwar Canji, an sayi Dalar Amurka a farashin N515 kuma an sayar a N523 ranar Laraba.
CBN kuwa a shafinta ta rubuta cewa farashin na nan a N410.16/$1.
Yaushe farashin ya fara fadi?
Jim kadan sanarwan da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele yayi na dakatar da sayar da Dala ga yan kasuwar canji, farashin Dalar ta tashi a kasuwar bayan fagge da na banki.
Alkaluman da aka gani a abokiFX.com, wata shafin da ke tattara farashin kudi a kasuwar bayan faggen Legas, sun nuna cewa a jiya farashin Dala ya tashi daga N504 da aka sayar ranar Litinin zuwa N505.00.
Hakazalika, farashin Naira ta fadi a kasuwar bankuna ranar Talata kamar yadda alkaluman da aka daura kan FMDQ suka nuna.
CBN ta haramta sayar da Dala ga yan kasuwan canji daga yanzu
Babbar bankin Najeriya CBN ya haramta sayar da Dalar Amurka ga yan kasuwan canji (BDC).
Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan zaman kwamitin kudi MPC na bankin ranar Talata, rahoton DailyTrust.
Ya ce N5. 7 billion da ake baiwa yan kasuwar canji ba zai yiwu a iya cigaba ba saboda kimanin yan kasuwan canji 5500 ake baiwa $110million kowani mako.
Ra'ayin Masana
Legit ta zanta da wani ma'aikacin wani babban banki a Najeriya, Mr Yusuf Abdullateef, wanda ya bayyana ra'ayinsa kan wannan sabon sanarwa na bankin CBN.
A cewarsa, wannan mataki ne da ya dace illa akwai wasu kalubale da hasashen matsaloli dake tattare da hakan.
Yace:
"Ni a ra'ayin abune mai kyau a mayar farashin sayar da Dala guda daya kacal sabanin yadda abin yake inda banki ya banbanta da na kasuwar fagge, amma shin CBN zai samar da isasshen Dala ga bankuna don sayarwa mutane?."
"Yan kasuwan canji ne yanzu fa ke sayarwa mutane Dala saboda CBN ta hana sayarwa daidaikun mutane Dalar Amurka na tsawon lokaci yanzu, illa manyan kamfanoni masu bukatar shigo da kaya, sai kuma masu son biyan kudin makarantar yaransu dake kasashen waje."
"Matsalar dai yanzu shine farashin canjin Naira zuwa Dala zai tashi na dan lokaci a kasuwar bayan fagge."
Asali: Legit.ng