Hadimin Buhari ya yi wa PDP mugun baki, ya ce Jam’iyyar za ta shiga tsilla-tsilla kafin zaben 2023
- Gwamnonin jam’iyyar PDP sun ce APC ta dauki Aso Villa wajen taron Jam’iyyar
- Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya maida wa Gwamnonin na PDP martani
- Adesina ya ce PDP ta rika shirya taro a Aso Villa lokacin da ta ke mulkin Najeriya
Abuja - Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce PDP za ta shiga cikin fagamniya da rudani yayin da aka dumfari zaben 2023.
Jaridar The Cable ta rahoto Femi Adesina ya na cewa jam’iyyar hamayyar za ta rasa ‘ya ‘yanta.
A ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, 2021, gwamnonin PDP suka fito suna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya maida Aso Rock sakatariyar APC.
Femi Adesina ya yi wa Gwamnonin jam’iyyar PDP raddi
Da yake magana a ranar Talata inda yake maida masu martani, hadimin shugaban kasar Najeriya ya ce PDP ta rika yin taro a Aso Villa yayin da ta ke mulki.
Femi Adesina ya yi hira da wani talabijin daga Ingila, ya ce jam’iyyar adawar ta na rasa ‘ya ‘yanta, don haka babu abin da ba za ta fada ba, ko da bai da ma’ana.
“Daga yanzu zuwa 2023, za a samu karin rudani a tafiyarsu (jam’iyyar PDP), za kuma a samu wasu suna ta ficewa, shiyasa za su iya fadan komai.”
PDP ta rika shirya taro a Aso Villa daga 1999 zuwa 2015
“Muna kasar nan lokacin da shugaba Olusegun Obasanjo ya ke mulki, kuma aka rika yin taron kwamitin amintattun jam’iyyar PDP a fadar Aso Villa.”
“Muna nan a sa’ilin da ‘Yar’adua, shugaba Jonathan su ke kan mulki, suka rika shirya taro a cikin fadar shugaban kasa. Maganar me suke nema su yi?”
Adesina ya ce zafin rasa jihohin da suke mulki ne ya sa PDP ke maganganun da ya ce sokiburutsu ne.
“Lokacin da APC ta rasa gwamnoni daga 24 zuwa 19, ka ji APC ta na kuka? Duk don saboda ta na rasa goyon baya ne, shiyasa ta ke wannan surutan.”
Bayanan sirri za su daina barin fadar shugaban kasa
A jiya ma’aikatan fadar Aso Rock suka dauki rantsuwa cewa za su tsare sirrin Gwamnati. Gwamnati za ta dauki mataki a kan wanda aka samu ya saba doka.
An kawo wani Alkali ya lakkana wa Ma’aikatan rantsuwa a fadar Shugaban kasa, tare da jan-kunnen duk wani da aka samu ya na tozarta gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng