Babu yunkurin sa Gwamna Ganduje ya hana mata tuka mota a Kano inji Dr. Sani Rijiyar Lemu
- Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu ya karyata jita-jitar hana mata tuka mota
- Babban malamin ya ce rade-radin da ake ji na wannan yunkuri ba gaskiya ba ne
- Sheikh Sani Umar Rijiyar-Lemu yace wasu makiya ne suka kirkiri labarin bogin
Kano - Wasu daga cikin manyan malaman jihar Kano sun fitar da sanarwa, inda suka yi fatali da rade-radin da ake ji na yunkurin hana mata tuka mota.
Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu, daya ne daga cikin jiga-jigan malaman jihar Kano, ya fitar da sanarwa ta musamman, ya na karyata jita-jitar.
A wani bayani da Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu ya fitar a zauren karatunsa na Telegram da shafinsa na yanar gizo, ya ce labarin ba gaskiya ba ne.
Babban malamin ya yi wa sanarwar ta ke da ‘Jan hankali’, ya ce har da sunansa cikin wadanda ake karyar sun bukaci a hana mata tuka mota a jihar Kano.
A wannan sanarwa da ta fito ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021 (18 ga watan Zul Hajj), malamin ya yi kira ga al’ummar Kano su yi watsi da karyayyakin.
Dr. Sani Umar Rijiyar-Lemu ya fitar da gajeren sanarwar da harshen Hausa da Ingilishi, ya ce wasu makiya ne suka kirkiri labarin domin bata masa suna.
Titsiye Abduljabbar Kabara bai yi wa wasu dadi ba
A cewar malamin, wasu mabiya shi’a da ba su ji dadin yadda ta kasance da Sheikh Abduljabbar Kabara a wajen mukabala kwanaki ba ne suke ta yada jita-jitar.
Malamin ya fitar da wannan sanarwa ta jan hankalin har a shafinsa na Facebook a yammacin Laraba.
Jawabin jan hankali daga Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu
“Mun ga wani labarin karya da ake yadawa cewa, wai wasu malamai a Kano, daga cikinsu har da ni, sun gabatar wa da Gwamnatin Kano kudurin hana mata tukin mota a Kano.”
Wannan labari, bisa dukkan alamu, wasu ne daga cikin Shi'a wadanda ba su ji dadin titsiyen da aka yi wa Abduljabbar ba suka tsara shi, suke kuma yadawa.”
“A yi watsi da wannan labari domin tsatsuniya ne ba gaskiya ba. Allah ya kare mu daga sharrin makiya Allah. Amin.”
Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara
Kwanaki aka ji lauyoyin Abduljabbar Nasir Kabara su na ce gwamnatin Kano ta na yi wa shari’ar da ake yi da shehin malamin addinin musuluncin katsalandan.
Barista Saleh M. Bakaro, wanda yake kare Sheikh Abduljabbar Kabara, ya ce bai kamata Gwamnan Kano ya rika magana yayin da magana ta ke kotu ba.
Asali: Legit.ng