Kungiya ta na lallabar ‘Yar’adua ya fito takarar Gwamnan jihar Katsina a 2023

Kungiya ta na lallabar ‘Yar’adua ya fito takarar Gwamnan jihar Katsina a 2023

  • Wasu mutane suna zuga Abubakar Sadiq Yar’Adua ya yi takarar Gwamna a 2023
  • Aliyu Danmusa ya ce Sanata Abubakar Yar’Adua zai dace da Gwamnan Katsina
  • Masu goyon-bayan ‘Dan siyasar sun ce yayi abin a yaba da ya zama ‘Dan Majalisa

Katsina - Mazauna garin Kaduna ‘yan asalin jihar Katsina sun roki Abubakar Sadiq Yar’Adua ya fito neman takarar gwamnan Katsina a zabe mai zuwa.

Mutanen na jihar Katsina suna so Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua ya ceto jihar daga halin da ta shiga.

Aliyu Danmusa ya na tare da Abubakar Sadiq Yar’Adua

Da ya yi hira da The Nation a garin Kaduna, shugaban kungiyar ta ‘yan asalin Katsina, Aliyu Danmusa ya ce Sadiq Yar’Adua ya fi dace wa da jiharsu.

Danmusa ya na ganin kokarin da Abubakar Sadiq Yar’Adua yayi da ya ke majalisar wakilai da ta dattawa sun sa ya yi zarra a cikin ‘yan siyasan Katsina.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gidan ya cabe, bangaren Lai Mohammed sun sa sharadin barin APC

“Duk da ya yi wata hira kwanan nan inda ya ce lokaci bai yi ba da zai bayyana niyyar takararsa, mu na rokonsa ya yi la’akari da matasan da su ke kiran shi domin ya zo ya yi ceto.”

Abin da ya sa mu ke rokon 'Yar'adua ya nemi kujerar Gwamna

“Gwamna mai-ci, Aminu Bello Masari ya yi kokari sosai, don haka ake bukatar mutum da ya dace irin Sanata ‘Yar’adua ya zama magajinsa, ya cigaba da ayyukan da ya riga ya fara.”

APC a Jihar Katsina
Buhari a wajen kamfe a APC Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

“Kwanan nan ya gina gidan marayu, ya damka wa kungiyar JNI domin daukar dawainiyar marayu a jihar.”
“Baya ga haka ga ayyukan cigaban da ya kawo a lokacin da yake Sanata a majalisar dattawa, wanda har yanzu babu wanda ya iya kamo kafan irin abin da ya yi.”

Danmusa ya fada wa jaridar madadin daukacin mutanen da ke zama a Katsina da asalin ‘yan jihar a wasu garuruwan, suna yin kira ga Sanata ‘Yar’adua ya fito takara.

Kara karanta wannan

Wani sabon yamutsi ya na jiran Shugabannin APC a kan yadda za ayi rabon kujeru na kasa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga cikin masu harin kujerar gwamnan jihar Katsina a 2023 akwai Mustafa Inuwa, Sanata Ahmad Babba-Kaita, da Ahmad Kangiwa.

A baya kun ji cewa Mai girma gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya ce ilimi ne zai iya zama maganin 'yan ta'addan dake addabar jihohin kasar nan.

Da yake bayani ta bakin Ibrahim Musa-Kalla, Gwamnan ya yi kira da a sanya hannun jari mai yawa ga ilimtar da matasa domin a magance rashin tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel