2023: Jam’iyyar PDP ta bayyana lokaci da dalilin da zai sa manyan APC su yi ta sauya-sheka

2023: Jam’iyyar PDP ta bayyana lokaci da dalilin da zai sa manyan APC su yi ta sauya-sheka

  • PDP ta na ganin rikicin cikin gida zai raba kan APC bayan zabukan da za ta yi
  • Diran Odeyemi ya na sa rai Jiga-jigan Jam’iyyar APC za su nemi su dawo PDP
  • Jigon na PDP ya ce akwai yiwuwar Umahi da Matawalle su bar APC kafin 2023

Jam’iyyar PDP mai adawa ta ce gwamnoni, sanatoci da wasu manyan da ke APC, za su sauya-sheka nan gaba, Daily Trust ta fitar da wannan rahoton.

Za a rika ficewa daga Jam'iyyar APC kafin 2023 - PDP

Jam’iyyar ta ce wadannan mutane za su fice daga APC mai mulki bayan ta shirya taron gangami na kasa, inda za a zabi wadanda za su rike mukamai.

Jaridar ta rahoto jam’iyyar PDP ta na mai sa ran wasu daga cikin gwamnonin da suka bar ta, suka koma APC za su gamu da bakin ciki kafin zaben 2023.

Mataimakin sakataren yada labarai na PDP na kasa, Diran Odeyemi ya yi magana da ‘yan jarida a waya, ya ce akwai yiwuwar PDP ta karbe mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi karin bayani a kan yadda ‘Dan takarar Shugaban kasan 2023 zai fito

“Don wasu suna barin jam’iyya ba ya barin za ta mutu. Jam’iyya za ta kai labari. Wasu sun bar ta a baya, a karshe suka dawo, kuma PDP ta na nan abinta.”

Diran Odeyemi ya ce ka da ayi la’akari da abubuwan da suka faru domin hakan ba zai canza komai ba.

Jam’iyyar APC
Buhari a Osun wajen kamfe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Har ila yau, Odeyemi ya yi fashin-baki a game da sauyin shekar gwamnan jihar Ebonyi da na Zamfara, ya ce gwamnonin na iya neman su koma PDP.

“Kuma wanene ya fada maku a lokacin da APC ta kammala zabukanta da gangami na kasa, wasu gwamnoni ba za su fusata, su dawo jam’iyyar PDP ba.”
“Gwamna Umahi ya tafi ne saboda tunanin APC za ta kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu maso gabas. Idan hakan ba ta yiwu ba, zai iya dawo wa PDP.”
“Dayan gwamnan ya ce ya sauya-sheka ne saboda ya taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari wajen yakar rashin tsaro a jihar, da zarar ya fahimci talakawa ba su kaunar jam’iyyar APC, zai iya koma wa PDP.”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

A gefe guda, kun samu labari cewa shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar APC za su gamu da kalubale yayin da wasu ‘yan takara su ka ce dole a shirya zabe.

‘Yan takarar sun ce ta hanyar shirya zabe ne za a fitar da wadanda za su rike mukamai. Irinsu George Akume ba su yarda a kakaba shugabanni haka kawai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel