Bayan kwanaki 23 a garkame, Alkali ta bukaci a fito da masu zanga-zangar #BuhariMustGo

Bayan kwanaki 23 a garkame, Alkali ta bukaci a fito da masu zanga-zangar #BuhariMustGo

  • Alkali ta umarci DSS su saki masu zanga-zangar ‘BuhariMustGo’ da suke tsare
  • A ranar Litinin aka saurari shari’ar wadannan mutane da DSS a birnin tarayya
  • Za a koma kotu a Agusta, amma kafin nan an ce jami’an tsaro su saki mutanen

Babban kotun tarayya da ke garin Abuja ta ba hukumar DSS umarni ta saki mutane biyar da ta kama kwanaki a coci suna sanye da rigunan ‘BuhariMustGo’.

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, 2021, Alkali Anwuli Chikere ya saurari karar da aka kai masa, sannan ya zartar da wannan hukuncin.

Anwuli Chikere ta ce jami’an tsaro su daina tsare wadannan Bayin Allah, su fito da su kafin ranar da kotu za ta sake zama, an dage karar zuwa 2 ga watan Agusta.

DSS ta saba doka inji Lauya

Lauyan ya ce tsare mutanen da yake kare wa da aka yi, ya saba bangarori na 35, 38, 39, 42 na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Har ila yau, Lauyan ya ce DSS ta saba sassa na 1, 2, 6, 8, da 9 da dokar kare hakkin Bil Adama a Afrika.

Rahoton ya ce lauyan da ya tsaya wa wadanda aka tsare, Tope Temokun Esq., ya shigar da kara, inda ya shaida wa kotu cewa an shiga hakkin wadannan mutane.

Masu zanga-zangar #BuhariMustGo
'Yan ‘BuhariMustGo’ Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Premium Times ta ce Alkalin ta karbi korafin Temokun, ta bada umarnin a fito da mutanen cikin gaggawa tun da hukumar DSS ba ta tuhume su da wani laifi ba.

Su wanene wadannan mutane da aka kama?

An cafke Ben Manasseh, Anene Udoka, Henry Nwodo, Samuel Larry da Samuel Gabriel kwanaki ne a cocin Dunamis International Gospel Centre, a garin Abuja.

Wadannan mutane biyar da ke tsare a hannun DSS sun bukaci a biya kowanensu kudi Naira miliyan goma, saboda ci masu zarafi da aka yi, domin su rage zafi.

Ben Manasseh, Anene Udoka, Henry Nwodo, Samuel Larry da Samuel Gabriel suna cikin ‘yan tafiyar #RevolutionNow, da Omoyele Sowore ya kafa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zamfara, Jihohin Arewa ne kan gaba yayin da ‘Yan bindiga suka harbe mutum 1031 a kwana 30

Asali: Legit.ng

Online view pixel