Jam'iyyar APC ta yi karin bayani a kan yadda ‘Dan takarar Shugaban kasan 2023 zai fito

Jam'iyyar APC ta yi karin bayani a kan yadda ‘Dan takarar Shugaban kasan 2023 zai fito

  • Jam’iyyar APC ta yi karin-haske game da yadda za ta shiga takara a zaben 2023
  • APC ta ce za a bi dokar kasa da tsarin mulkin jam’iyya wajen fito da ‘Dan takara
  • Wasu sun fara zargin ana kokarin yi masu karfa-karfa wajen neman takaran 2023

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba za ta kakaba daya daga cikin manyan ‘ya ‘yanta a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto jam’iyyar ta na bayanin yadda ‘dan takarar ta zai fito a zaben 2023.

A baya ne babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta fito ta na zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya na da shirin cigaba da mulki bayan wa’adinsa ya cika.

APC ta maida martani, ta na mai cewa ta na shirin yin zabukan shugabanni a kowane mataki, ta ce za a fito da yadda za a bada tikitin takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta cire rai a zaben 2023

Jam’iyyar APC ta ce za ta yi babban gangami, inda a nan za a fito da ‘dan takarar da ake ganin shi ne maslaha, ya rike wa jam’iyya tuta a zaben shugaban kasa.

Rahoton ya ce jawabin da uwar jam’iyya ta yi ya soma kawo hayaniya, inda wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar suke ganin ana shirin kakaba ‘dan takara ne.

Sakataren rikon kwarya na APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya bayyana cewa za su fito da ‘yan takara a 2023 yadda dokar jam’iyya ta tanada.

Mai Mala Buni
Shugaban rikon kwarya na Jam'iyyar APC
Asali: Facebook
“Kamar yadda tsarin siyasa yake, idan lokaci yayi da za a tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da sauran ‘yan takara, za a bi kundin tsarin mulkin 1999 sau-da-kafa.”
“Za a bi matakin kamar yadda dokar kasa da tsarin mulkin APC na fitar da ‘yan takara ta ce.”
“APC ta na da tsarin mulki, ta yadda za a fito da ‘dan takara ta hanyar zaben fitar da gwani, ko kuma idan ta kama a tsaida ‘dan takara, ayi masa mubaya’a.”

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Yari ya ce wasu 'Yan siyasan Arewa na kokarin hana shi zama Shugaban APC

Domin ayi karin-haske, APC ta ce tunanin da wasu ke yi na za ayi rashin adalci a 2023, ba haka be ne.

A jiya kun ji cewa jagoran PDP, Segun Sowunmi yana ganin karon Bola Tinubu ko Gwamna Yahaya Bello ba za ta yi wa jam'iyyar PDP kyau a zabe mai zuwa ba.

'Dan siyasar ya na ganin Tinubu da Gwamnan na Kogi ne kadai za su iya ba PDP ciwon kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel