'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Katsina, Sun Yi Kisa Sun Kuma Sace Dabbobi 300 da Babura

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Katsina, Sun Yi Kisa Sun Kuma Sace Dabbobi 300 da Babura

  • 'Yan bindiga sun kai hari garin Kukar Babangida da ke karamar hukumar Jibia a Katsina
  • Mazauna garin sun tabbatar da harin inda suka ce an kashe mutum daya an raunata uku
  • Yayin harin, yan bindigan sun sace dabobi kimanin 300 da babura da tufafi da wasu kayayyaki

'Yan bindiga a ranar Lahadi sun kai hari garin Kukar Babangida a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina inda suka kashe mutum daya suka raunata wasu uku, Premium Times ta ruwaito.

Mazauna garin sun ce yan bindigan sun isa garin misalin karfe 11 na dare, suka rika harbe-harbe a yayin da suke shiga gidaje suna neman dabobi da sauran abubuwa masu daraja da za su sace.

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Katsina, Sun Yi Kisa Sun Kuma Sace Dabbobi 300 da Babura
Taswirar jihar Katsina. Hoto: The Punch
Asali: UGC

A yayin da suka kammala, yan bindigan sun sace kimanin dabobi 300 da babura da tufafi a cewar mazauna garin da dama da suka nemi a boye sunayensu saboda tsaro.

Mazauna garin sun tabbatar da harin

Majiyar ya ce:

"Sun zo misalin karfe 11 na dare, suka rika shiga gida-gida suna neman dabobbi. Sun bindige mutum daya har lahira sannan suka raunata mutum uku. An birne wanda suka kashe a safiyar ranar Litinin."

Ya kara da cewa mutanen uku da aka yi wa rauni suna wani asibiti suna samun kulawa.

Abin da yasa aka saka wa garin suna Kukar Babangida

Kukar Babangida, wani gari ne da ke hanyar Katsina zuwa Jibia da a baya mutane kan tafi can domin tsira daga harin yan bindiga.

An canja sunan garin ne aka nada sunan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida, a lokacin da ya ziyarci garin ya shuka wani bishiya yayin ziyarar aiki da ya kai a 1980s.

Lambar kakakin yan sandan jihar Katsina Gambo Isah bai shiga ba a safiyar ranar Litinin yayin da wakilin Premium Times ya yi kokarin tuntubarsa game da lamarin.

'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel