Kwankwaso ya ba Jam’iyyar PDP umarni ta binciki na-kusa da shi kan zargin shirya zagon-kasa
- Ana binciken wasu limaman Kwankwasiyya kan zargin cin amana da zagon-kasa
- Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi PDP ta binciki wadannan zargi
- Yunusa Dangwani da Yusuf Dambatta su na cikin wadanda ake zargi da laifuffuka
Politics Digest ta kawo rahoto cewa jam’iyyar PDP ta reshen jihar Kano ta kafa wani kwamitin ladabtar wa da zai binciki wasu kusoshin tafiyar Kwankwasiyya,
Jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi za ta binciki zargin da ke kan wuyan Dr. Yunusa Adamu Dangwani da kuma Hon. Yusuf Bello Dambatta.
Jaridar ta bayyana cewa an kafa wannan kwamitin ne bayan wani Bawan Allah mai suna Ahmed Sani Maidaji ya gabatar da korafi kan Yusuf Bello Dambatta.
Dr. Yunusa Adamu Dangwani ya rike shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da kwamishinan harkar ruwa a lokacin da Rabiu Kwankwaso yake gwamnan Kano.
Yunusa Adamu Dangwani ya bayyana gaban kwamiti
A ranar Alhamis ne Dr. Dangwani ya bayyana a gaban wannan kwamiti domin amsa tambayoyi a kan zargin yi wa jam’iyyar PDP da kuma jagoran na ta zagon-kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin Dangwani a matsayin ‘yan gaba-gaba a tafiyar siyasar Kwankwasiyya a jihar Kano, amma akwai zargin sabani tsakaninsa da Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Daga cikin korafin da ake yi shi ne Yunusa Adamu Dangwani ba ya tare da Abba Kabir Yusuf, duk da shi ne ya yi masa darektan yakin neman zaben gwamna a 2019.
Haka zalika Yusuf Bello Danbatta ya bayyana a gaban wannan kwamiti. Danbatta ya yi wa Kwankwaso kwamishinan kasafi da tattalin arziki, da na safiyo a baya.
Dambatta ya na cikin hadiman Sanata Rabiu Kwankwaso a lokacin da yake majalisar dattawa. Shi ma ya na cikin wadanda ake zargi suna harin takarar gwamna a 2023.
Kwamitin da shugaban jam'iyyar PDP ya kafa
‘Yan kwamitin ladabtarwan da jam'iyyar adawar ta kafa domin wannan aiki sun hada da; Hashimu Dungurawa, Dahiru A. Dakata, Hafiz Bunkure, da Binta Kofar Ruwa.
Ragowar ‘yan kwamitin su ne; Halima Uba Jalli, Jamilu Kabo da Barista Wangida da zai yi aiki a matsayin sakatare.
A ranar Lahadin da ta wuce ne aka ji cewa masu kare Sheikh Abduljabbar Kabara sun yi wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje raddi bayan ya yi maganganu da sallah.
Gwamnan Kano ya yi wasu kalamai yayin da Sheikh Abduljabbar Kabara ya ke a daure, wanda lauyoyi suke ganin za su iya yin tasiri a shari'ar da ake yi da shehin malamin.
Asali: Legit.ng