Ana tare: Dattijon Sarkin Yarbawa ya tada tawaga zuwa kasar Benin a halarci shari’ar Igboho

Ana tare: Dattijon Sarkin Yarbawa ya tada tawaga zuwa kasar Benin a halarci shari’ar Igboho

  • Oba Saliu Adetunji ya tura mutanen da za su saurari shari’ar Sunday Igboho
  • Sarkin kasar Ibadan ya ce akwai bukatar a kare Cif Sunday Adeyemo a kotu
  • Kwanaki ne aka cafke Igboho a kasar Benin, ya na yunkurin barin Afrika

Mai martaba Olubadan na kasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji, ya tura tawaga ta musamman zuwa Cotonou, kasar Benin, domin sauraron shari’ar Sunday Adeyemo.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa tawagar da Sarki Saliu Adetunji ya tada, za ta halarci zaman shari’ar da za ayi da Sunday Igboho a birnin Cotonou a yau dinnan.

Oba Saliu Adetunji ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar ta bakin hadiminsa, Adeola Oloko.

Rahoton ya ce Sarkin bai bayyana sunayen wadanda aka tura zuwa kasar ketaren ba, amma ya tabbatar da cewa wakilan na sa za su hallara a kotu a ranar Litinin.

Oloko ya ce Oba Adetunji ya yi wannan jawabi ne a fadarsa da ke Ibadan, a lokacin da ya zauna da wasu manyan kasar Yarbawa a jiya, ranar 25 ga watan Yuli, 2021.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Wadanda su ka gana da Sarkin sun hada da; Yemisi Adeaga, Dr Tirimisiyu Oladimeji; Ekefa Olubadan, Lekan Alabi; Ajia Olubadan, Wasiu Aderoju Alaadorin; Mogaji Makusota, da Oluwasegun Adekunle.

Sarkin Ibadan
Oba Saliu Adetunji Olubadan Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Sarkin ya ce akwai bukatar ya dauki mataki game da lamarin Sunday Igboho da abokan tafiyarsa.

“Sunday Igboho ya na zaune a Ibadan, ya yi aure a Ibadan, ya haihu a Ibadan, ya gina gidaje a Ibadan, don haka ya cancanci masarautun Ibadan, su bi dokar kasa, su kare shi kamar kowane mutum a Ibadan.”

Oba Adetunji ya ce ya na ta tuntubar sauran Sarakunan Yarbawa domin gudun abin da ya faru tsakanin Fulani da Yarbawa a shekarar 1814 ya sake maimaita kansa.

Jaridar ta ce Mai martaba, Adetunji ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, ya ce gaskiya za ta fito.

Rahotanni sun ce Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya fara tunanin tsige Mai martaba Sarkin Misau saboda ya shirya wani taro ba tare da izinin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa

Gwamnatin APC ce ta nada Ahmed Sulaiman bayan ya rike Sakataren Gwamnatin Jiha. Bayan PDP ta karbi mulki a 2019, Sarkin ya rika samun matsala da gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel